Dakarun Sojojin Najeriya sun ragargaji 'yan fashi a Katsina-Ala, sun kashe guda 3

Dakarun Sojojin Najeriya sun ragargaji 'yan fashi a Katsina-Ala, sun kashe guda 3

- Rundunar Operation Whirl Stroke sun kai hari kan sansanin miyagun da ke kauyukan Tomatar Ugba da Kundi

- A yayin wannan aiki sun kashe yan ta’addan guda uku sannan suka kama wasu hudu

- Sun yi nasarar kai wannan farmaki ne bayan samun wasu bayanai na sirri a kan miyagun

Dakarun rundunar sojin Najeriya na Operation WHIRL STROKE, a safiyar ranar Asabar, 12 ga watan Disamba, sun kai mamaya wasu maboyar yan bindiga a kauyukan Tomatar Ugba da Kundi da ke karamar hukumar Katsina Ala na jihar Benue.

Sun dauki wannan matakin ne bayan samun rahotanni na sirri kan miyagun.

Dakarun sojin sun kai farmaki sansanonin, sannan suka yi musayar wuta inda suka sha kan miyagun ta hanyar yi masu barin wuta.

Dakarun Sojojin Najeriya sun ragargaji 'yan fashi a Katsina-Ala, sun kashe guda 3
Dakarun Sojojin Najeriya sun ragargaji 'yan fashi a Katsina-Ala, sun kashe guda 3 Hoto: @DefenceInfoNG
Asali: Twitter

Hakan ya tursasa yan ta’addan tserewa, kamar yadda hedikwatar tsaro ta sojojin ta wallafa a shafinta na Twitter.

KU KARANTA KUMA: Hotuna da bidiyo daga wajen auren dan tsohon shugaban kasa Obasanjo

Sai dai kuma sojojin sun bi sahun yan ta’addan da suka tsere sannan suka kashe mutum uku a cikinsu yayinda wasu da dama suka tsere da raunuka na harbin bindiga.

Har ila yau, sojojin sun kama wasu hudu bayan da sojojin suka bi sahun wadanda suka tsere.

Sun kuma samo manyan bindigu na gargajiya biyu, karamar bindigar gargajiya daya, alburasai 16, babura biyu, janareto uku, kayan sojoji biyu, tabar wiwi da yawa da dai sauransu.

A yanzu dakarun sun mamaye yankin domin yin fatrol sosai sannan kuma suna bibiyar sahun yan bindigan da suka tsere domin su gano su tare da halaka su.

An kuma bukaci jama’a da su ci gaba da ba rundunar sojin muhimman bayanai kan yan ta’addan.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Gwamnatin Katsina ta rufe dukkanin makarantun jihar har sai baba ta gani

A wani labarin, hedikwatar rundunar tsaro (DHQ) ta baza sojojin kasa da na sama domin nemowa da kuma kubutar da daliban makarantar sakandiren kimiyya ta Kankara, jihar Katsina, da 'yan bindiga suka sace, kamar yadda HumAnge ta rawaito.

HumAngle ta rawaito cewa kakakin shugaban kasa, Garba Shehu, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar.

A wasu 'yan shekaru da suka gabata ne rundunar sojin sama ta kaddamar da wani sansani na musamman (FOB) a Katsina da kuma wata cibiyar mayar ta martanin gaggawa (QRW) a Daura.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng