Yanzu Yanzu: Mata na zanga zanga a Katsina kan satar yaran makarantar GSSS Kankara

Yanzu Yanzu: Mata na zanga zanga a Katsina kan satar yaran makarantar GSSS Kankara

- Mata sun gudanar da zanga zanga a jihar Katsina kan sace yaran makarantar GSSS Kankara

- An gudanar da gangamin ne a yau Lahadi, 13 ga watan Disamba, a harabar makarantar da titunan yankin

- Har ila yau gamayyar kungiyoyin arewa sun yi barazanar tara dalibai da matasan domin yin zanga zanga idan har ba a ceto yaran ba

Wani rahoto daga jaridar Punch ya nuna cewa an gudanar da zanga zanga a jihar Katsina a ranar Lahadi, 13 ga watan Disamba kan sace daliban makarantar sakandare na kimiya ta gwamnati da ke Kankara, karamar hukumar Kankara ta jihar.

Masu zanga zangar na neman ayi gaggawan ceto daliban da wasu yan bindiga suka yi garkuwa da su a daren ranar Juma’a, 11 ga watan Disamba.

Wata mata wacce ta bayyana kanta a matsayin daya daga cikin iyayen daliban da aka sace ita ce ta jagoranci zanga zangar.

Yanzu Yanzu: Mata na zanga zanga a Katsina kan satar yaran makarantar GSSS Kankara
Yanzu Yanzu: Mata na zanga zanga a Katsina kan satar yaran makarantar GSSS KankaraHoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Dakarun Sojojin Najeriya sun ragargaji 'yan fashi a Katsina-Ala, sun kashe guda 3

Masu zanga zangar sun kewaye harabar makarantar da wasu yankunan garin dauke da kwalayen sanarwa da sakonni daban-daban kamar irinsu: ‘Ya zama dole gwamnati ta yi maggana’, ‘muna so a dawo mana da yaranmu’ da kuma ‘muna son tsaro a Kankara.’

Har ila yau masu zanga zangar na ta wake-waken neman a ceto daliban da aka sace.

A halin da ake ciki, gamayyar kungiyoyin arewa sun yi barazanar tattara dalibai da matasan domin yin zanga zanga a jihar Katsina idan har ba a ceto yaran da aka sace a kan lokaci ba.

Shugaban kungiyar reshen arewa maso yamma, Jamiu Aliyu wanda ya zanta da taron manema labarai a Katsina ya ce: “Mun yi Allah wadai da wannan rashin imanin sannan muna kira ga kama masu laifin cikin gaggawa tare da hukuntasu. Sannan muna Allah wadai da gazawar gwamnati wajen ba wadannan yaran bayin Allah da basu ji ba basu gani ba kariya daga wannan mummunan hari.

“Idan har gwamnati ta gaza ceto daliban da aka sace cikin dan kankanin lokaci, CNG ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen tattara dubban daruruwan dalibai ba domin ci gaba da zanga zanga, har sai an ceto yaran, koda kuwa za mu rasa ranmu ne.”

KU KARANTA KUMA: Hotuna da bidiyo daga wajen auren dan tsohon shugaban kasa Obasanjo

A gefe guda, Gwamnatin jihar Katsina ta sanar da rufe dukkanin makarantu a jihar tare da kawo karshen zangon karatu na uku daga ranar Asabar 12 ga watan Disamba.

Har ila yau gwamnati ta umurci dukkanin makarantu kama daga na gwamnati har masu zaman kansu a kan su ci gaba da rufe makaranta har sai baba ta gani.

Wannan sanarwar na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na ma’aikatar ilimi ta jihar Katsina, Sani Danjuma Suleiman ya fitar wanda Legit.ng ta gano.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel