Hotuna: Soja ya rasu, 2 sun jigata bayan yunkurin Boko Haram na kwace Askira Uba
- Rundunar sojin sama tana cigaba da samun nasarori mabambanta a arewa maso gabas
- A ranar 12 ga watan Disamba rundunar OLD ta ragargaji wasu 'yan Boko Haram a jihar Borno
- Sun samu nasarar kwace miyagun makamai a hannunsu, ciki harda motocin yaki guda 15
Rundunar sojin Najeriya sun saki wasu hotuna, wadanda suke nuna miyagun makamai da suka kwace daga hannun mayakan Boko Haram lokacin wani karon batta da suka yi a arewa maso gabas a ranar 12 ga watan Disamban 2020.
Kungiyar Boko Haram sun kai wani hari zuwa karamar hukumar Askira Uba da ke arewa maso gabashin Najeriya, sai dai tarkonsu bai kama kurciya ba, a cewar sojojin.
Mataimakin shugaban jami'in hulda da jama'a na Division 7 da ke rundunar sojin Najeriya a Maiduguri, Kanal Ado Isa, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata takarda da ya fitar ranar Lahadi.
KU KARANTA: Hadimin Buhari ya goyi bayan Zulum da dalilai, ya ce Borno ta samu cigaban tsaro
Ya ce ana zargin 'yan ta'addan sunbullo ne daga dajin Sambisa inda suka tunkari bangarori daban-daban na garin a kan wasu motocin yaki guda 15.
Sai dai rundunar Operation Lafiya Dole sun dakatar dasu daga shiga garin, inda suka hau ragargazar su suka yi musu kaca-kaca, Channels Tv ta wallafa.
KU KARANTA: Yajin aiki: Mun cika wa ASUU dukkan alkawurran da muka dauka, FG
A wani labari na daban, a ranar Lahadi gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya ce har yanzu ba a ga dalibai 333 ba na makarantar sakandare ta kimiyya da ke Kankara, Punch ta wallafa.
Ya bayyana hakan lokacin da ministan tsaro, janar Salihi Magashi, ya jagoranci shugabannin tsaro zuwa jihar Katsina don yi wa gwamnan jaje a kan satar daliban makarantar sakandare da aka yi ranar Juma'a a jihar Katsina.
Wadanda suka kai ziyarar sun hada da shugaban jami'an tsaro, shugaban sojojin sama da sauransu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng