Laolu Akande ya ce Gwamnatin Tarayya za ta fara aikin gina gidaje 300, 000

Laolu Akande ya ce Gwamnatin Tarayya za ta fara aikin gina gidaje 300, 000

-Gwamnatin Tarayya za ta gina gidaje 300, 000 na masu karamin karfi

-Za a gina wadannan gidaje a jihohi 20, gwamnoninsu sun bada filayen

-Laolu Akande ya ce za a saida gida mai cin daki daya kan N1.8m-N2m

Babban mai taimaka wa mataimakin shugaban kasa wajen yada labarai, Laolu Akande yace gwamnatin tarayya ta yi shirin gina gidaje 300, 000.

A ranar Lahadin nan, Laolu Akande ya bayyana cewa za a soma wannan aiki ne a makon nan.

Punch ta rahoto hadimin fadar shugaban kasar ya na wannan bayani a ranar Litinin, 14 ga watan Disamba, 2020.

Wannan gine-gine da za a yi, ya na cikin tsarin bada muhalli da gwamnatin Muhammadu Buhari ta shigo da shi domin farfado da tattalin arzikin kasa.

KU KARANTA: Sarkin Ife ya bude gidauniyar da za ta rika tura Matasa karatu

“Kusan jihohi 20 suka nuna sha’awarsu ga tsarin ESP na gina gidajen ‘yan Najeriya 300, 000 a kan farashi N2m." Jaridar ta rahoto Akande ya na jawabi.

“A makon an za a bude shafin da masu bukatar su amfana da wadannan gidaje ko su yi aiki da gwamnatin tarayya wajen gina gidaje za suyi rajista.”

A cewar Akande, jihohin da su ka nuna sha’awarsu ga wannan tsari, sun bada kyautar filayen da za ayi wannan aiki da kananan ma’aikata za su amfana.

Hadimin na Farfesa Yemi Osinbajo ya ce za a saida gidajen ne da araha; daga N1.8m zuwa N2m.

KU KARANTA: Wani daga cikin wadanda su ka shirya zanga-zangar #EndSARS ya shiga hannu

Laolu Akande ya ce Gwamnatin Tarayya za ta fara aikin gina gidaje 300, 000
Laolu Akande da Mai gidansa Yemi Osinbajo Hoto: @ProfOsinbajo
Source: Twitter

Jaridar Punch ta ce jihohin da za a gina gidajen su ne: Osun, Ogun, Enugu, Delta, Bauchi, Kebbi, Nasarawa, Filato da kuma babban birnin tarayya, FCT.

Ya ce sauran jihohi irinsu Abia, Anambra, Ebonyi, Imo, Kuros Riba, Sokoto, Kaduna, Zamfara, Katsina, Borno da Yobe States su na yunkurin shiga sahu.

Dazu kun ji cewa duk da kashe-kashen da ake fuskanta a yau, babban malamin kungiyar Izala, Sani Yahaya Jingir yana ganin kokarin Muhammadu Buhari.

Sheikh Sani Jingir yace halin da ake ciki yau a Najeriya, bai kai munin abin da aka baro a baya ba, inda mutane su ka rika rayuwa a cikin firgici da tsoro.

Gara yanzu a kan da inji Shugaban malaman na Jama’atu Izalatil Bid’a Waikamatis Sunnah.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel