EndSARS: Jami’an DSS sun cafke Emmanuel Adebayo ‘Captain’ a Jihar Osun

EndSARS: Jami’an DSS sun cafke Emmanuel Adebayo ‘Captain’ a Jihar Osun

- Jami’an tsaro na DSS sun kama wani jagoran masu zanga-zangar #EndSARS

- A tsakiyar makon nan aka kira Emmanuel Adebayo, ba a sake jin labarinsa ba

- An fi sanin Emmanuel Adebayo da Captain a cikin garin Osogbo, jihar Osun

Wani shugaban ‘yan zanga-zangar #EndSARS a jihar Osun, ya samu kan shi a hannun jami’an tsaro bayan zanga-zangar ta su ta dawo danya.

Jaridar The Nation ta fitar da rahoto cewa jami’an hukumar DSS masu fararen kaya sun kama Emmanuel Adebayo wanda aka fi sani da Captain.

Jami’an DSS suna zargin Emmanuel Adebayo da laifin zama sojan gona bayan an kawo korafin cewa yana yawo da sunan shi jami’in sojan kasa ne.

Rahotonni sun ce hakan na zuwa ne bayan Mista Adebayo ya jagoranci sabuwar zanga-zangar da aka yi a ranar Litinin, 14 ga watan Disamba, 2020.

KU KARANTA: Shugabannin addini su ka jawo barkowar COVID-19 – PTF

Adebayo ya sa matasa a gaba inda su ka yi zanga-zanga a garin Osogbo, har su kayi tattaki zuwa majalisar dokoki domin yin tir da aikin 'yan sanda.

Wani jagora a wannan tafiya, Femi Farombi Jnr, ya tabbatar da cewa DSS sun gayyaci Adebayo domin amsa wasu tambayoyi, har yanzu yana hannunsu.

“(DSS) sun gayyace shi a ranar Talata. Ya fada mana Kolawole Amoo ya kira shi cewa ya zo ofishin DSS domin yayi bayani kan tafiyar #EndSARS.”

Femi Farombi ya ke bayani a ranar Alhamis, ya ce: “Ya amsa gayyatarsu, tun daga nan ba mu sake jin duriyarsa ba. Ya bar wa wani wayarsa kafin ya tafi”

KU KARANTA: Buhari ya bayyana irin dabarun da zai bi wajen yaki da talauci

EndSARS: Jami’an DSS sun cafke Emmanuel Adebayo ‘Captain’ a Jihar Osun
Masu zanga-zangar EndSARS Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Farombi yace a da suna waya da jami’an na DSS, amma daga baya sai suka daina daukar wayansu ko da an tuntube su domin jin halin wannan Bawan Allah.

A makon nan mun kawo maku mutane shida da suka buge da ‘karyar’ rashin lafiya yayin da su ka garfana a kotu inda ake binciken su da zargin aikata laifi.

Wasu ‘Yan siyasa su kan yi uzurin dole da ciwo bayan sun ji babu haza gaban Alkali ko majalisa. Daga cikinsu akwai Dino Melaye da Abdulrasheed Maina.

Irinsu Bello Halliru da Dino Melaye sun tattara sun tafi kotu da keken guragu ko cikin motar gawa

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel