Sarkin Ife ya kafa gidauniyar da za ta rika hidimar karatun miliyoyi a Jami’o’i

Sarkin Ife ya kafa gidauniyar da za ta rika hidimar karatun miliyoyi a Jami’o’i

-Ooni na kasar Ife ya kafa gidauniyar da za ta rika daukar nauyin karatun Matasa

-Wannan gidauniya za ta kashe N500bn a karatun dalibai biyar a kowace shekara

Arole Oduduwa kuma Ooni na Ife, Mai martaba Ooni Adeyeye Enitan Ogunwusi Ojaja II, sun kaddamar da wata gidauniya domin ba jama’a ilmi.

Daily Trust ta ce a ranar Laraba, 9 ga watan Disamba, 2020, aka kaddamar da wannan gidauniya da za ta dauki nauyin karatun yara har miliyan biyar.

Jaridar tace wannan gidauniya da Sarki Adeyeye Enitan Ogunwusi II ya kafa za ta dauki nauyin karatun jami’an mutane miliyan biyar duk a shekara.

Za a zakulo wadanda za su amfana da wannan gidauniya ne daga fadin jami’o’in da ke kasar nan.

KU KARANTA: ASUU ta c sai an biya mata bukatunta, za ta koma aiki

Burin mai martaba Adeyeye Enitan Ogunwusi shi ne ya ga yara sun shiga makaranta su samu ilmi, yana takaicin halin da wasu ‘yan makarantar su ke ciki.

Sarkin zai ware N50, 000 a kan kowane dalibi a shekara, za ayi shekaru hudu wannan gidauniya tana hidima ga wanda aka zaba, har su kammala karatun na su.

A kowace shekara wannan aiki da gidauniyar Mai martaban ta cincibo zai ci Naira biliyan 500.

Da Sarkin yake bayyana wannan shiri a fadar Oodua, yace Najeriya tana cikin babbar matsala muddin ba a ba matasa ilmi, an kuma inganta rayuwarsu ba.

KU KARANTA: An yi awon-gaba da Basarake bayan ‘Yan bindiga 20 sun shiga Neja

Sarkin Ife ya kafa gidauniyar da za ta rika hidimar karatun miliyoyi a Jami’o’i
Sarkin Ife Ooni Adeyeye Enitan Ogunwusi Ojaja Hoto: legit.ng
Asali: Original

Ya ce: “Na kafa wannan gidauniya ne domin tallafa wa kokarin da gwamnati ta ke yi…Gara mu gyara kasar nan, da mu rika kokarin tsere wa daga Najeriya.”

Ooni yace za a tuntubi attajiran mutane da kamfanoni da manyan kungiyoyi a Najeriya da kuma ketare domin a samu kudin da za ayi wannan gagarumin aiki.

A jiya kun ji cewa Dalibai sun koka game da yajin-aikin da ake ta yi a jami'o'i, sun yi barazanar zasu bi hanyar tsiya idan ta kama don a bude makarantun.

Sabon shugaban kungiyar dalibai da aka zaba ya nuna zai sa kafar wando daya da ASUU da gwamnatin tarayya kan yajin-aikin da ya ki, ya ki cinye wa.

NANS ta ce za ta garkame Jami’o’in kasuwan fadin kasar nan domin dalibai su daina zaman gida

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel