Rashin tsaro: Shugaban JIBIWIS, Jingir yace Buhari ya fi Shugabannin baya

Rashin tsaro: Shugaban JIBIWIS, Jingir yace Buhari ya fi Shugabannin baya

- Sheikh Sani Yahaya Jingir ya yi magana game da halin rashin tsaro da ake ciki

- Malamin yace duk abin da ke faruwa yau, an fuskanci abin da ya fi haka a baya

- Shugaban kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’a Waikamatis Sunnah ya bada shawara

Shugaban kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’a Waikamatis Sunnah na kasa, Sheikh Sani Yahaya Jingir, ya yabi shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.

Malamin yana ganin duk da kalubalen da gwamnatin nan take fuskanta na tsaro, Muhammadu Buhari ya zarce sauran shugabannin da suka shude a baya.

Jaridar Daily Trust ta ce Sheikh Sani Yahaya Jingir ya bayyana wannan ne a wajen taron gasar Al-Qur’ani ‘musabaqa’ na kasa da aka shirya a garin Gombe.

“Muna fama da manyan matsaloli na rashin tsaro a kasar nan, amma nayi imani cewa halin da ake ciki ya fi yadda ake a baya.” Inji Sheikh Sani Yahaya Jingir.

KU KARANTA: Za a dawo da yaran da aka sace a Katsina - Minista

Rashin tsaro: Shugaban JIBIWIS, Jingir yace Buhari ya fi Shugabannin baya
Malaman addini da Shugaban Najeriya Hoto: www.mediaissuesng.com
Asali: UGC

Sani Yahaya Jingir ya yi karin-haske, yace komai lalacewa, ba za a ce gara jiya a kan yau ba.

“Lokacin da ake tsoron hadu wa da juna a taro. Ba na cewa abubuwa duk sun yi kyau, amma an samu cigaba a sha’anin tsaro.” Malamin ya cigaba da bayani.

Bisa dukkan alamu, dattijon Malamin ya na nuni ne da lokacin da rikicin Boko Haram ya yi kamari, lokacin da aka rika zaman dar-dar saboda gudun tashin bam.

Sheikh Jingir, ya yi kira ga shugaban kasar ya canza salon yadda yake yaki da ‘yan ta’ada da tsagerun da su ka addabi Najeriya, domin a samu zaman lafiya.

KU KARANTA: Rashin tsaro: Dama na fada tuni, ba za a ga Buhari a Majalisa ba - Fayose

Ba wannan ne karon farko da aka ba gwamnatin tarayya shawarar ta canza salon yakin da ta ke yi ba, har ta kai ana kiran a tsige shugabanni da hafsohin tsaro.

A farkon shekarar nan idan za ku tuna, rundunar 'yan sandar jihar Filato ta kira shugaban majalisar koli ta malaman na JIBWIS domin ya amsa tambayoyi.

An tasa Sheikh Sani Yahaya Jingir a gaba ne a kan rashin biyayya ga umarnin jiha na hana dukkan wani taro saboda gujewa kamuwa da kwayar coronavirus.

Sheikh Jingir ya yi watsi da umarnin ya jagoranci sallah, amma daga baya ya canza ra'ayi.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel