Hotuna da bidiyo daga wajen auren dan tsohon shugaban kasa Obasanjo
- Tsohon Shugaban kasa Obasanjo ya shaida auren daya daga cikin yayansa
- Aure ya kullu a tsakanin Seun Obasanjo da kyakkyawar amaryarsa Deola Shonubi
- Legit.ng ta gano hotuna da bidiyon bikin wanda ya samu halartan manyan masu fada aji
Tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya cika da farin ciki irin wanda kowani uba da ke alfahari da haihuwa yake shiga yayinda ya shaidi auren daya daga cikin yaransa maza.
Dan tsohon Shugaban kasar, Seun, ya angwance da amaryarsa, Deola Shonubi, a ranar Asabar, 12 ga watan Disamba, a gaban yan uwa da abon arziki.
A gano wasu jerin hotuna na ma’auratan a shafin Instagram din shahararriyar mai kwalliyar nan ta zamani, Banke Meshida, inda aka gano amaryar da mahaifiyarta suna shiri na wannan babban rana.
Wasu hotunan aka gano a shafin soshiyal midiya ya nuna lokacin da mahaifin angon ya cakare tare da sabbin ma’auratan.
KU KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya taya Anthony Joshua murnar lashe wasan dambe da yayi a kan Pulev
Kalle su a kasa:
Sauran hotuna sun nuna yan uwa da abokan arziki wadanda suka hallara don taya su murna.
An kuma gabatar da wani kyauta na musamman na bazata ga amaryar.
KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Gwamnatin Katsina ta rufe dukkanin makarantun jihar har sai baba ta gani
An yi wa Deola kyautar mota kirar Mercedes Benz sabuwa dal. A wani bidiyon da ya bayyana a yanar gizo, an gano lokacin da amaryar wacce ke cike da farin ciki take duba sabuwar motarta sannan ta rungume wadanda ke wajen da aka yi mata kyautar.
Kalli bidiyon a kasa:
A wani labarin, a yau Lahadi 13 ga watan Disambar 2020 ne aka daura auren matashi dan jihar kano Isa Suleiman Panshekara da sahibarsa 'yar Amurka, Janine Sanchez.
Tsohon sanata mai wakiltan mazabar Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani ne waliyin amarya Janine Sanchez kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito.
Al'umma da dama sunyi tururuwa zuwa masallacin Juma'a na Gasau da ke karamar hukumar Kumbotso don shaida daurin auren da ake dade ana fatan ganin ranar bayan da masoyan biyun sun dauki lokaci suna soyaya.
Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng