An ɗaura auren Isa Panshekara da sahibarsa Ba'amurkiya a Kano (Hotuna)
- An daure aure tsakanin matashi dan Kano Isa Panshekara da amaryarsa 'yar Amurka Jenine Sanchez a Kano
- Masoyan biyu sun hadu ne a dandalin sada zumunta na Instagram bayan Isa ya ankarar da Jenine game da wasu da ke neman damfararta
- Daga bisani soyayya ta yi karfi har Jenine ta yi tattaki zuwa Nigeria ta gana da iyayen Isa kuma suka amince da auren
A yau Lahadi 13 ga watan Disambar 2020 ne aka daura auren matashi dan jihar kano Isa Suleiman Panshekara da sahibarsa 'yar Amurka, Janine Sanchez.
Tsohon sanata mai wakiltan mazabar Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani ne waliyin amarya Janine Sanchez kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito.
Al'umma da dama sunyi tururuwa zuwa masallacin Juma'a na Gasau da ke karamar hukumar Kumbotso don shaida daurin auren da ake dade ana fatan ganin ranar bayan da masoyan biyun sun dauki lokaci suna soyaya.
DUBA WANNAN: Hotuna: Ganduje ya tafi ta'aziyya Danbatta, ya bada N1.6m ga iyalan mutum 16 da suka rasu
Angon ya biya sadaki na Naira Dubu 50 lakadan ba ajalan ba.
Mahaifin ango Malam Suleiman a zantawar da ya yi da BBC ya ce an daura auren ne bayan an amince da dukkanin sharuddan da ya gindaya.
Cikin manyan bakin da suka halarci daurin auren sun hada da Sanata Shehu Sani da kuma shugaban karamar hukumar Kumbotso na Jihar Kano.
Hotunan daurin auren sun nuna dandazon al'umma sun hallarci daurin auren inda aka gano 'yan Hisbah na kokarin kulawa da shige da ficen mutane a wurin.
KU KARANTA: Adadin talakawan Nigeria zai kai miliyan 110 a ƙarshen shekarar 2020, inji Peter Obi
Jenine Sanchez ta fara soyayya da Suleiman Panshekara ne ta dandalin sada zumunta na Instagram bayan ya burge ta da gaskiyarsa ta hanyar ankarar da ita game da wasu 'yan damfarar intanet.
Anngo Isa ya ce iyayensa sun amince masa da auren masoyiyarsa Jenine kuma nan da watan Maris za a yi bikinsu daga bisani kuma su lula Amurka tare.
"Bayan bikin mu a watan Maris insha Allah, za mu wuce Amurka inda nake sa ran samun aiki ko na koma makaranta sannan in samu kungiyar da zan dinga buga wa kwallo", in ji shi.
A wani labarin daban, Shugaba Muhammadu Buhari ya sauke shugaban hukumar daukan ma'aikata, Dakta Nasiru Mohammed Ladan Argungu daga mukaminsa.
Sanarwar saukewar na kunshe ne cikin wata wallafa da babban mataimakin shugaban kasa a bangaren watsa labarai, Mallam Garba Shehu ya fitar a ranar Talata kamar yadda The Punch ta ruwaito.
Sanarwar ta ce Buhari ya umurci karamin ministan Kwadago da Ayyuka, Festus Keyamo, SAN, ya nada shugaban riko daga cikin manyan direktocin hukumar don maye gurbin Argungu a yanzu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng