Shugaba Buhari ya taya Anthony Joshua murnar lashe wasan dambe da yayi a kan Pulev

Shugaba Buhari ya taya Anthony Joshua murnar lashe wasan dambe da yayi a kan Pulev

- A daren ranar Asabar, 12 ga watan Disamba, Anthony Joshua yayi nasara a kan Kubrat Pulev a Landan

- Shugaba Buhari ya taya Anthony Joshua murnar hazikancin da ya nuna wajen yin nasara

- Joshua zai fuskanci Englishman Tyson Fury a was an dambe na gaba da zai yi

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya taya shahararren dan was an damben nan haifaffen kasar, Anthony Joshua murna bisa nasarar da yayi wajen doke Kubrat Pulev.

Anthony Joshua ya nuna bajinta a daren ranar Asabar, 12 ga watan Disamba, inda ya lallasa abokin adawarsa a karo na tara na babban was an damben.

Kafin damben, dan wasan na kasar Bulgaria Kubrat Pulev ya yi bayanin cewa a shirye yake ya doke Anthony Joshua wanda ya sha kasa a wasan da aka yi a Landan.

Shugaba Buhari ya taya Anthony Joshua murnar lashe wasan dambe da yayi a kan Pulev
Shugaba Buhari ya taya Anthony Joshua murnar lashe wasan dambe da yayi a kan Pulev Hoto: Andrew Couldridge
Source: Getty Images

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Gwamnatin Katsina ta rufe dukkanin makarantun jihar har sai baba ta gani

A cewar wata sanarwa daga mai ba Shugaba Buhari shawara a kafofin watsa labarai, Femi Adeshina, Shugaban kasar ya bayyana karara cewa Anthony Joshua ya yi bajinta.

Buhari ya kuma bayyana Anthony Joshua a matsayin mutum mai ƙanƙan da kai da kuma tarbiyya a lokacin da suka hadu a birnin Landan a farkon wannan shekarar.

Ya kuma yi ikirarin cewa dan was an damben zai yi nisa a rayuwa kan wannan aiki nasa.

Har ila yau, Buhari ya yi wa Joshua fatan alheri a damben da zai gwabza da Tyson Fury nan gaba, yana mai cewa addu'o'in 'yan Najeriya na tare da shi.

KU KARANTA KUMA: Harin yan bindiga: Yadda muka shafe tsawon dare a daji, Daliban GSSS Kankara

A wani labarin, Shugaba kasa Muhammadu Buhari ya naɗa sabon shugaban wucin gadi a hukumar NDDC.

Kakakin shugaban ƙasa ya ce an zaɓi Effiong Ikon Akwa a matsayin shugaban wucin gadin.

Sanarwar ta ce Akwa zai cigaba da jagorancin hukumar har zuwa lokacin da za a kammala binciken da ake yi Read more: https://hausa.legit.ng/1392095-buhari-ya-nada-shugaban-wucin-gadi-a-nddc.html

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel