Yanzu Yanzu: Gwamnatin Katsina ta rufe dukkanin makarantun jihar har sai baba ta gani

Yanzu Yanzu: Gwamnatin Katsina ta rufe dukkanin makarantun jihar har sai baba ta gani

- Gwamna Aminu Bello Masari ya yi umurnin rufe dukkanin makarantun jihar Katsina tare da kawo karshen zangon karatu na uku

- Wannan umurni ya shafi makarantun gwamnati da masu zaman kansu kuma zasu ci gaba da kasancewa a kulle har sai baba ta gani

- Matakin ya biyo bayan harin da yan bindiga suka kai makarantar GSSS da ke Kankara a jihar

Gwamnatin jihar Katsina ta sanar da rufe dukkanin makarantu a jihar tare da kawo karshen zangon karatu na uku daga ranar Asabar 12 ga watan Disamba.

Har ila yau gwamnati ta umurci dukkanin makarantu kama daga na gwamnati har masu zaman kansu a kan su ci gaba da rufe makaranta har sai baba ta gani.

Wannan sanarwar na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na ma’aikatar ilimi ta jihar Katsina, Sani Danjuma Suleiman ya fitar wanda Legit.ng ta gano.

Yanzu Yanzu: Gwamnatin Katsina ta rufe dukkanin makarantun jihar har sai baba ta gani
Yanzu Yanzu: Gwamnatin Katsina ta rufe dukkanin makarantun jihar har sai baba ta gani Hoto: @GovernorMasari
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Harin yan bindiga: Yadda muka shafe tsawon dare a daji, Daliban GSSS Kankara

Jawabin ya zo kamar haka:

"SANARWA! SANARWA!! SANARWA!!!

“Wannan sakon don sanar da al’umma musamman shugabannin makarantu, iyaye, wakilai, jagororin garuruwa da makarantu masu zaman kansu cewa, zangon karatu na uku na 2019/2020 ya zo karshe daga ranar Asabar 12 ga watan Disamba, 2020.

“Don haka, ana umurtan dukkanin makarantun gwamnati da masu zaman kansu a kan su ci gaba da kasancewa a kulle har sai baba ta gani.

“Daga Sani Danjuma Suleiman, jami’in hulda da jama’a na ma’aikatar ilimi. Jihar Katsina.”

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da wasu yan bindiga suka kai hari makarantar GSSS da ke Kankara ta jihar a daren ranar Juma’a, 11 ga watan Disamba.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Daruruwan daliban da aka yi awon gaba da su a makarantar sakandare a Katsina sun dawo

A baya mun ji cewa sakamakon harin da yan bindiga suka kai makarantar sakandaren gwamnati dake karamar hukumar Kankara a jihar Katsina, gwamna Aminu Bello Masari, ya bada umurnin kulle dukkan makarantun kwanan jihar.

Gwamnan ya bada umurnin ne yayin magana da manema labarai bayan ziyarar da ya kai makarantan ranar Asabar, Vanguard ta ruwaito.

Masari ya ce a kulle makarantun kuma dalibai su koma gidajensu.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel