2023: Jigo a APC ya bayyana mutanen da za su fitar da yankin shugaban kasa

2023: Jigo a APC ya bayyana mutanen da za su fitar da yankin shugaban kasa

- Kashim Shettima ya ce an yi gaggawar fara magana a kan wanda zai tsaya takarar shugaban kasa a APC a 2023

- Tsohon gwamnan jihar Borno ya ce shugabannin jam'iyya, har da Buhari za su zauna su tattauna a kan lamarin

- Shettima ya tabbatar wa da duniya cewa jam'iyyar APC za ta yi nasara a zaben 2023, ta cigaba da mulki

Kashim Shettima, tsohon gwamnan jihar Borno, ya ce ya yi wuri shugabannin APC su fara magana a kan zaben shugaban kasa na 2023.

Ya fadi hakan ne a Ado Ekiti, babban birnin jihar Ekiti a ranar Juma'a, 4 ga watan Disamba yayin wani zaman tattaunawa na masu ruwa da tsakin jam'iyyar APC

Kashim ya bayyana hakan, inda yace ana karkatar da hankulan shugabanni a kan abubuwan da ke faruwa a kasa a halin yanzu.

KU KARANTA: Fitaccen dan kasuwa, hamshakin mai kudi kuma tsohon dan takarar shugaban kasa ya rasu

2023: Jigo a APC ya bayyana mutanen da za su fitar da yankin shugaban kasa
2023: Jigo a APC ya bayyana mutanen da za su fitar da yankin shugaban kasa. Hoto daga @KashimSM
Asali: Twitter

Shettima ya ce idan lokacin yazo, shugabannin APC har da Shugaban kasa Muhammadu Buhari da Bola Ahmed Tinubu, tsohon gwamnan jihar Legas, za su taru su zabi wanda jam'iyya za ta tsayar a takarar shugaban kasa.

Legit.ng ta tattaro bayanai a kan yadda tsohon gwamna, wanda yayi magana da ministan ayyuka da gidaje, Raji Fashola, inda suka tabbatar da cewa APC ba za ta rabe ba saboda takarar shugaban kasar 2023.

Kashim Shettima ya bayyana yadda yake da tabbaci a kan APC za ta samu nasara a 2023.

Kamar yadda yace, "Kada ku manta jam'iyyarmu ita ce take mulki. Muna da shugabanni wadanda za su iya dakatar da duk wani rikici da ka iya barkewa."

Yace "Idan lokacin da ya dace yayi, shugabanninmu za su zauna su tsayar da wanda ya kamata ya tsaya takara."

KU KARANTA: Hotunan ranar daurin auren jarumi Nuhu Abdullahi da zukekiyar amaryarsa

A wani labari na daban, wasu mutane dauke da makamai da ake zargin 'yan bindiga ne sun tarwatsa masu kada kuri'a a kauyen Oroji da ke gundumar Rini ta karamar hukumar Bakura da ke jihar Zamfara a ranar Asabar.

Lamarin ya faru a ranar Asabar yayin da ake zaben maye gurbi na majalisar dattawa, kamar yadda rahoto daga HumAngle ya bayyana.

Jaridar Daily Trust ta bayyana yadda wani mai kada kuri'a mai suna Sulaiman Muhammad, yake sanar da cewa lamarin ya faru wurin karfe 8:30 na safe yayin da ake dab da fara saka kuri'u.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
APC
Online view pixel