Sojoji sun gano inda ƴan bindiga suka ɓoye ɗaliban GSSS Kankara, anyi musayar wuta

Sojoji sun gano inda ƴan bindiga suka ɓoye ɗaliban GSSS Kankara, anyi musayar wuta

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da harin da yan bindiga suka kai makarantar GSSS Kankara

- An tattaro cewa sojojin Najeriya sun gano inda ƴan bindiga suka ɓoye harma sun yi musayar wuta

- Ana ci gaba da kokarin ganin an gano ko dalibai nawa aka yi garkuwa da su

Rahotanni sun nuna cewa rundunar sojojin Najeriya da taimakon dakarun sama sun yi nasarar gano mabuyar ƴan bindigan da suka kai farmaki makarantar sakandare na kimiya ta gwamnati da ke Kankara, jihar Katsina.

An gano cewa ƴan bindigan sun boye ne a dajin Zango/Paula da ke karamar hukumar ta Kankara harma an yi musayar wuta tsakaninsu da sojoji.

Kakakin Shugaban kasa, Mallam Garba Shehu ne ya sanar da wannan ci gaban a cikin wata sanarwa da ya saki wanda Legit.ng ta gano.

Sojoji sun gano inda ƴan bindiga suka ɓoye ɗaliban GSSS Kankara, anyi musayar wuta
Sojoji sun gano inda ƴan bindiga suka ɓoye ɗaliban GSSS Kankara, anyi musayar wuta Hoto: @dailynigerian
Source: Twitter

KU KARANTA KUMA: An saki dan majalisan jihar Taraba da yan bindgiga suka sace

Ya bayyana cewa shugaba Muhammadu Buhari ya samu labarin haka ne a wani jawabi daga Gwamna Aminu Bello Masari da kuma Shugaban hafsan soji, Janar Tukur Buratai.

Sannan kuma ya ce a bangaren yan sanda sun ce har yanzu ba a samu rahoton mutuwar kowani dalibi ba.

Har ila yau, Shehu ya bayyana cewa Buhari ya yi Allah wadai da harin ƴan bindigan a kan makarantar.

Ya kuma bukaci rundunar soji da na yan sanda a kan su bi sahun maharan don tabbatar da ganin ba kowani dalibi da ya bata ko ya cutu.

“Ina matukar yin Allah wadai da harin da matsorata suka kai kan bayin Allah yaran makarantar kimiya ta Kankara da basu ji ba basu gani ba. Addu’anmu na tare da iyayen daliban, hukumomin makarantar da kuma wadanda suka jikkata,” in ji Shugaban kasar yayinda ya dauki alwashin ci gaba da ba yan sanda da sojoji gudunmawa a yaki da suke da yan ta’adda.

Shugaban kasar ya bukaci hukumomin makarantar da su gudanar da kidayar dalibai sakamakon harbe-harbe da aka yi a ciki da kewayen makarantar wanda ya sa dubban mutane tarwatsewa.

Daga karshe an bukaci iyayen da suka yi gaggawan zuwa makarantar sannan suka tafi da yaransu a kan su sanar da makarantar da hukumomin yan sanda domin a samu cikakken bayani kan adadin daliban makarantar.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Daruruwan daliban da aka yi awon gaba da su a makarantar sakandare a Katsina sun dawo

A gefe guda, sakamakon harin da yan bindiga suka kai makarantar sakandaren gwamnati dake karamar hukumar Kankara a jihar Katsina, gwamna Aminu Bello Masari, ya bada umurnin kulle dukkan makarantun kwanan jihar.

Gwamnan ya bada umurnin ne yayin magana da manema labarai bayan ziyarar da ya kai makarantan ranar Asabar, Vanguard ta ruwaito.

Masari ya ce a kulle makarantun kuma dalibai su koma gidajensu.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel