An saki dan majalisan jihar Taraba da yan bindgiga suka sace
- Bayan kwanaki a hannun masu garkuwa da mutane, dan majalisa ya samu kubuta
- Yan bindigan sun bukaci iyalinsa sun biya kudin fansan N150m
- Hukumar yan sandan ta tabbatar da sakin dan majalisan amma ba'a bayyana nawa a biya ba
Dan majalisar dokokin jihar Taraba, Bashir Bape, da aka yi garkuwa da shi ya samu yanci a daren Juma'a, majiya daga hukumar yan sanda da iyalansa sun tabbatar.
A cewar rahoton Premium Times, har yanzu ba a san ainihin adadin kudin da aka biya kudin fansa ba amma majiya daga gidan dan majalisan ya bayyana cewa: "an biya kudin fansa kafin aka sakeshi."
"An sake shi a daren jiya misalin karfe 10 na dare, kuma yanzu yana asibiti. Muna godiya ga dukkan wadanda suka taya mu addu'a," ya kara.
Yayinda aka tuntubi kakakin hukumar yan sanda a jihar, David Misal, ya tabbatar da lamarin.
"Mun tabbatar da cewa an sake shi," Misal yace.
Dubi ga yadda garkuwa da mutane ke yawaita a jihar, gwamnatin jihar ta haramta hawa babur a Jalingo da kewaye.
Kakakin gwamnan jihar, Iliye Bikye, ya ce an haramta hawa babur din ne saboda da babura ake amfani wajen aika-aika.
KU KARANTA: Yan ta'adda sun yi awon gaba da Ango da abokinsa bayan daurin aure
DUBA NAN: Harin Kankara: Gwamna Masari ya kulle dukkan makarantun kwana a jihar Katsina
Mun kawo muku cewa wadanda suka sace Bashir Muhammed, dan majalisa a majalisar dokokin jihar Taraba, sun bukaci a biya naira miliyan 150 kafin su sake shi.
An sace Muhammed, wanda ke wakiltan mazabar Nguroje a karamar hukumar Sardauna da ke jihar, a gidansa da ke Jalingo a ranar Laraba, 9 ga watan Disamba.
A cewar rahoton, Muhammed ya roki shugabannin majalisar dokokin Taraba da gwamnatin jihar a kan su biya bukatar wadanda suka sace shi domin ceto rayuwarsa.
A cewar wata majiya a rahoton, mambobin majalisar sun hadu da Gwamna Darius Ishaku kan lamarin.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng