'Yan bindiga sun yi awon gaba da dumbin dalibai a makarantar sakandire a Katsina

'Yan bindiga sun yi awon gaba da dumbin dalibai a makarantar sakandire a Katsina

- Labarin da duminsa na nuni da cewa 'yan bindiga sun yi awon gaba da dumbin dalibai daga dakinsu na kwana a makarantar Sakandiren Kankara

- Ya zuwa yanzu ba'a san adadin daliban da 'yan bindigar suka tafi da su daga makarantar ba

- Ana suraron fitowar jawabin rundunar 'yan sanda ko wata hukumar tsaro daga jihar Katsina

Labari da dumi-duminsa da Legit.ng Hausa ta samu jaridar HumAngle ya bayyana cewa wasu 'yan bindiga sun yi awon gaba da dumbin dalibai daga wata makarantar sakandire ta kimiyya da ke karamar hukumar Kankara a jihar Katsina.

A cewar HumAngle, 'yan bindigar sun shiga har dakin kwanan daliban tare da yin awon gaba da su da duku-dukun safiyar yau, Asabar.

HumAngle ta wallafa cewa ana kidayar adadin daliban da aka sace a yayin da ta wallafa labarin da dumi-dumi a shafinta na sada zumunta; tuwita.

KARANTA: Sakon Bidiyo: A karo na biyu; El-Rufa'i ya sake killace kansa saboda annobar korona

"Da duminsa: 'Yan bindiga sun dira makarantar sakandiren kimiyya da ke karamar hukumar Kankara a jihar Katsina, arewa maso yammacin Nigeria, tare da yin awon gaba da dumbin dalibai daga dakinsu na kwana da sanyin safiyar yau. Ana cigaba da kidayar adadin daliban da 'ya bindigar suka sace," kamar yadda HumAngle ta wallafa a tuwita.

'Yan bindiga sun yi awon gaba da dumbin dalibai a makarantar sakandire a Katsina
'Yan bindiga sun yi awon gaba da dumbin dalibai a makarantar sakandire a Katsina @Punch
Asali: Twitter

Jihar Katsina na daga ckin jihohin arewa maso yammacin Nigeria da ke fama da matsalar 'yan bindiga.

'Yan bindiga na cigaba da kai hare-hare a sassan jihar duk da yawan jamu'an tsaro da aka tura da kuma atisaye daban-daban da suka kaddamar a yankin.

A baya, gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya taba yin sulhu da 'yan bindiga domin a samu zaman lafiya.

KARANTA: Bidiyon Sheikh Karibu Kabara: Ina ajiye da zirin gashin Annabi da aka bani kyauta shekaru 8 da suka gabata

Sai dai, sulhun bai yi wani tasiri ba, saboda 'yan bindiga sun cigaba da kai hare-hare tare da kisan mutane babu gaira, babu dalili, tare da yin awon gaba da dukiyoyinsu.

Bayan asarar rayuka da dukiyoyin al'umma, 'yan bindiga na sace mutane tare da yin garkuwa da su domi neman kudin fansa.

Wanna shine karo na farko da rahoto ya bayyana cewa 'yan bindigar sun shiga makarantar kwana tare da yin awon gaba da dumbin dalibai a jihar Katsina.

A ranar Juma'a ne Legit.ng Hausa ta wallafa rahoton cewa kotun ICC mai tuhumar manyan laifukan ta'addanci da cin zarafin jama'a ta ce za ta binciki hukumomin tsaron Nigeria.

Mai gurfanarwa a kotun ta ce ofshinta ya na kwararan hujjoji na zahiri da za'a iya kimantasu a kan jami'an hukumomin tsaron Nigeria.

Fatou Bensouda, mai gurfanarwa da ke shirin barin gado, ta lissafa wasu manyan laifuka da ICC ke zargin jami'an tsaron da aikatawa.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel