Shugaba Buhari ya yi jimamin mutuwar mawallafin jaridar Leadership Sam Nda-Isaiah
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aika sakon ta’aziyyarsa a kan mutuwar shahararren dan jarida Sam Nda-Isaiah
- Shugaban kasar ya bayyana Nda-Isaiah a matsayin aboki kuma makusanci wanda ya yarda da Najeriya mai inganci
- Nda-Isaiah, babban ginshikin kasar ya mutu yana da shekaru 58 a duniya
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika ta’aziyyarsa ga bangaren labarai, abokai, da kuma yan uwan Sam Nda-Isaiah kan mutuwar shahararren jigon kasar.
Shugaban Najeriyan yayinda yake nuna kaduwa da bakin ciki kan mutuwar mawallafin jaridar na Leadershi, ya bayyana Nda-Isaiah a matsayin aboki kuma makusanci.
Legit.ng ta tattaro cewa hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa a ranar Asabar, 12 ga watan Disamba, daga mai ba Shugaban kasar shawara a kafofin watsa labarai, Mallam Garba Shehu.
KU KARANTA KUMA: Wadanda suka yi garkuwa da dan majalisar Taraba sun nemi a biya miliyan 150 kudin fansa
A wani sakon ta’aziyya, Shugaba Buhari ya bayyana cewa Najeriya ta yi rashi na mutum mai yarda da kudiri kan ingancin Najeriya.
Ya ci gaba da bayyana cewa shakka babu za a yi kewar tsohon dan takarar Shugaban kasar na jam’iyyar All Progressives Congress (APC).
Shugaba Buhari ya ce “Wannan babban kifi ne ya tafi a kogin kafofin watsa labarai.”
A baya mun ji cewa Allah ya yi wa mawallafin Jaridar Leadership, Mista Sam Nda-Isaiah rasuwa yana da shekaru 58 a duniya.
Majiyoyi sun bayyana wa The Nation cewa marigayin ya rasu misalin ƙarfe 10 na daren ranar Juma'a bayan ya koka kan cewa baya jin daɗin jikinsa.
KU KARANTA KUMA: Halima Abubakar: Likita yar arewa da ke neman miji a shafin soshiyal midiya
Nda-Isiah ya hallarci taron kungiyar masu jaridu ta Najeriya, NPAN, a jihar Legas a ƙarshen mako.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng