Wadanda suka yi garkuwa da dan majalisar Taraba sun nemi a biya miliyan 150 kudin fansa

Wadanda suka yi garkuwa da dan majalisar Taraba sun nemi a biya miliyan 150 kudin fansa

- Masu garkuwa da mutanen da suka sace Honourable Bashir Muhammed sun bukaci a biya naira miliyan 150 kafin su sake shi

- Honourable Muhammed ya kasance mamba a majalisar dokokin jihar Taraba

- Wasu yan bindiga ne suka sace dan majalisar a gidansa da ke Jalingo, babbar birnin jihar Taraba a ranar Laraba, 9 ga watan Disamba

Wani rahoto daga jaridar Daily Trust ya nuna cewa wadanda suka sace Bashir Muhammed, dan majalisa a majalisar dokokin jihar Taraba, sun bukaci a biya naira miliyan 150 kafin su sake shi.

An sace Muhammed, wanda ke wakiltan mazabar Nguroje a karamar hukumar Sardauna da ke jihar, a gidansa da ke Jalingo a ranar Laraba, 9 ga watan Disamba.

A cewar rahoton, Muhammed ya roki shugabannin majalisar dokokin Taraba da gwamnatin jihar a kan su biya bukatar wadanda suka sace shi domin ceto rayuwarsa.

Wadanda suka yi garkuwa da dan majalisar Taraba sun nemi a biya miliyan 150 kudin fansa
Wadanda suka yi garkuwa da dan majalisar Taraba sun nemi a biya miliyan 150 kudin fansa Hoto: @tarabagovt
Asali: UGC

KU KARANTA KUMA: Halima Abubakar: Likita yar arewa da ke neman miji a shafin soshiyal midiya

A cewar wata majiya a rahoton, mambobin majalisar sun hadu da Gwamna Darius Ishaku kan lamarin.

A baya mun kawo maku cewa 'Yan bindiga da ake kyautata zaton masu garkuwa ne sun sace dan majalisar Jihar Taraba, Bashir Mohammed.

An sace Mohammed wanda ke wakiltar mazabar Nguroje a majalisar jihar misalin karfe 1 na daren ranar Laraba a Jalingo babban birnin jihar Taraba.

KU KARANTA KUMA: Gayyatar Buhari: Daga karshe majalisa ta magantu, ta bayyana dalilin gayyatar Shugaban kasar

The Cable ta ruwaito cewa an sace dan majalisar ne a gidansa da ke kusa da ofishin hukumar 'yan sandan farin kaya DSS.

A wani labarin, Mutanen da basu gaza mutane 16 yan asalin karamar hukumar Danbatta ne suka gamu da ajalinsu a babban titin Kaduna zuwa Abuja, Vanguard ta ruwaito.

Wata majiya daga karamar hukumar Danbatta, wanda yayi bayani cikin bacin rai, ya ce wanda suka rasa ran nasu duk maza ne, sun rasu ranar Talata lokacin da yan bindiga su ka harbi tayar motar su lokacin da take dauko su daga Abuja don dawowa Kano.

Majiyar ta shaida cewa lamarin ne yayi sanadiyar hadarin da ya janyo mutuwar mutanen.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng