Gayyatar Buhari: Daga karshe majalisa ta magantu, ta bayyana dalilin gayyatar Shugaban kasar

Gayyatar Buhari: Daga karshe majalisa ta magantu, ta bayyana dalilin gayyatar Shugaban kasar

- Benjamin Kalu, mai magana da yawun majalisar wakilai, ya yi bayani kan dalilinsu na gayyatar shugaba Buhari

- Gayyatar wanda majalisar ta yi wa Shugaban kasar ya janyo cece-kuce a tsakanin yan Najeriya

- Kalu ya bayyana cewa yan majalisar basa nufin yi wa Buhari ba’a a kan rashin tsaro

Mai magana da yawun majalisar wakilai, Kalu ya ce gayyatar da aka mika wa shugaban kasa Muhammadu Buhari ba wai an shirya shi don yi masa ba’a akan lamarin tsaro bane.

Vanguard ta ruwaito cewa Kalu ya fadi hakan ne yayinda yake zantawa da manema labarai a Abuja a ranar Alhamis, 10 ga watan Disamba.

Ya bayyana cewa maimakon haka, an gayyaci shugaban kasar n le domin ya tattauna da majalisa kan mafita don magance matsalolin tsaro a kasar.

Gayyatar Buhari: Daga karshe majalisa ta magantu, ta bayyana dalilin gayyatar Shugaban kasar
Gayyatar Buhari: Daga karshe majalisa ta magantu, ta bayyana dalilin gayyatar Shugaban kasar Hoto: @femigbaja
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Jarumar Kannywood Rahama Sadau ta shiga cikin jerin mutanen da suka fi tashe a intanet a 2020

Ya kuma ce manufar gayyatar shine domin jin bayanai kan halin da tsaron kasar ke ciki, inda ya kara da cewa za a ci gaba da rike hadin gwiwa tsakanin majalisar dokokin ta tara da bangaren zartarwa.

Sai dai yace tunda Najeriya na gudanar da mulki ne a kan tafarkin damokradiyya, Shugaban kasar na iya yanke hukuncin bin shawarar jam’iyyarsa a kan kowani lamari.

“Shugaban kasar ya fi jam’iyyar iko, amma idan ya dauki shawara daban sannan jam’iyyarsa ta dauki nata daban, dole ne ya bi jam’iyyar,” in ji shi.

Kalu ya bayyana cewa majalisar baya yi kuskure ba ta hanyar gayyatan shugaban kasar, inda ya kara da cewa jam’iyyar na da yancin yin bincike a kan lamuran da suka addabi kasar.

KU KARANTA KUMA: Manyan dalilai 6 da ke sa yan Najeriya barin kasarsu zuwa kasashen ketare

A gefe guda, shugaba Muhammadu Buhari ya ki amsa gayyatar da yan majalisar wakilan tarayya suka yi masa domin musu jawabi kan tabarbarewan tsaro a fadin tarayya.

Yayinda aka fara zama a zauren majalisa ranar Alhamis, ba a ga alaman shugaba Buhari ba, Channels TV ta ruwaito.

Wani dan majalisa daga jihar Rivers, Solomon Bon, ya yi tambaya kan dalilin da ya sa har yanzu shugaban kasan bai gurfana ba. Ya bukaci Kakakin majalisa yayi musu bayani.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng