An sace ɗan majalisa a jihar Taraba

An sace ɗan majalisa a jihar Taraba

- 'Yan bindiga sun yi garkuwa da dan majalisar jihar Taraba, Honarabul Bashir Mohammed

- 'Yan bindigan sun bi Mohammed har gidansa ne a cikin dare suka yi awon gaba da shi

- Rundunar 'yan sandan jihar Taraba ta tabbatar da afkuwar lamarin inda tace tana kokarin ceto shi

'Yan bindiga da ake kyautata zaton masu garkuwa ne sun sace dan majalisar Jihar Taraba, Bashir Mohammed.

An sace Mohammed wanda ke wakiltar mazabar Nguroje a majalisar jihar misalin karfe 1 na daren ranar Laraba a Jalingo babban birnin jihar Taraba.

The Cable ta ruwaito cewa an sace dan majalisar ne a gidansa da ke kusa da ofishin hukumar 'yan sandan farin kaya DSS.

An sace ɗan majalisa a jihar Taraba
An sace ɗan majalisa a jihar Taraba. Hoto daga @thecableng
Source: Twitter

DUBA WANNAN: ASUU ta amince za ta janye yajin aiki ranar 9 ga watan Disamba, inji Ngige

Rahotanni sun ce 'yan bindigan sun shafe kimanin mintuna 45 suna harbe harbe a yayin da suka afka gidansa.

Wata majiya tace yan bindigan ba su taba kowa ba a gidan dan majalisar.

Dan majalisar shine mai magana da yawun majalisar jihar a halin yanzu.

Da aka tuntube shi, kakakin 'yan sandan jihar Taraba, David Misal ya ce rundunar tana kokarin ganin ta ceto Mohammed.

KU KARANTA: Buhari ya sallami shugaban Hukumar NDE, Ladan Argungun

"Mun san abinda ya faru kuma muna kokarin ganin mun ceto shi," a cewar Misal cikin sakon kar ta kwana da ta aike wa majiyar Legit.ng.

A wani labrin daban, kwamitin zartarwa na jam'iyyar APC mai mulki a ranar Talata ya janye sharadin takara ga wanda suka shiga ko suke shirin shiga jam'iyyar.

Sharadin zai bada damar tsayawa takara a duk wata kujerar mulki ba tare da la'akari da dadewa a jam'iyyar ba.

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ne ya bayyana haka ga majalisa bayan kammala taron kwamitin kamar yada The Punch ta ruwaito.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel