AYCC ta bukaci Shugaban kasa yayi waje da Hafsun Soji da Babatunde Fashola
- Kungiyar AYCC ta yi Allah-wadai da halin rashin tsaro a Arewacin Najeriya
- AYCC tayi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sauke Hafsun soji
- Matasan suna so a sallami Raji Fashola a dalilin nawar aikin titin Abuja-Kano
A ranar Litinin, 7 ga watan Disamba, 2020, kungiyar The Arewa Youth Consultative Council (AYCC) ta fito ta koka game da sha’anin rashin tsaro.
Wannan kungiya ta matasan Arewacin Najeriya ta na so a tsige duka shugabannin hafsoshin tsaron Najeriya, a nada kwararru masu jini a jika.
Kungiyar tana so a nada zakuraran hafsun soji masu karfi da za su iya shawo kan matsalar tsaro. AYCC tana so ayi hakan ba tare da bata lokaci ba.
AYCC ta bakin shugabanta na kasa, Zaid Ayuba Alhaji, tace hafsun sojojin Najeriya sun gaza kawo zaman lafiya. The Nation ta fitar da wannan rahoto.
KU KARANTA: 'Yan Sanda sun mutu wajen aikin zaben Majalisa a Bayelsa
Zaid Ayuba Alhaji ya yi wannan jawabi ne gaban manema labarai a dakin taron nan na Aminu Kano Mambayya House da ke garin Kano, jihar Kano.
Wannan kungiya har wa yau, ta nemi shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya cire Ministan aiki da gidaje, Babatunde Raji Fashola daga kujerarsa.
“Shi kuma Babatunde Raji Fashola SAN, laifinsa shi ne ya gaza gyara babban tittin Abuja zuwa Kano, wanda wannan yake jawo hadura a kullum.”
Ayuba Alhaji yake cewa mutanen Arewa suna mutuwa kullu-yaumin a kan wannan babbar hanya, sannan kuma ana fama da garkuwa da mutane.
KU KARANTA: 'Yan bindiga sun sa Mutanen Sokoto sun koma kasar Nijar
AYCC tace za a iya gama aikin nan kafin 2021. “A sallami Babatunde Raji Fashola, za a iya kai shi wata ma’aikatar, amma ba ta ayyuka da gidaje ba.”
A farkon makon nan da ake ciki, kun ji cewa wata kungiya ta Mutanen Borno sunyi wa Boko Haram rubdugun addu’o’i 41, 000, 000 a zama guda.
Kungiyar Mutanen Borno ta zabga ruwan addu’o’i ta aikawa Boko Haram domin Allah ya kawo saukin matsalar tsaro, har dabbobi aka yanka a taron.
Har ila yau AYCC tana so a gyara titin Jalingo-Numan, ayi aikin Mambilla Hydropower Electric. Sannan ASUU ta janye aikin da take yi, a koma karatu.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng