Ba na nuna kabilanci: Amaechi ya magantu a kan barin Jonathan da goyawa Buhari baya
- Chibuike Amaechi na shirin dawowa da karfi domin kwato harkokin siyasa a jihar Ribas a 2021
- Tsohon gwamnan na jihar ya bugi kirjin cewa idan ya dawo, zai murza kambun domin duk abunda ya fadi zai kasance haka
- A cewar Amaechi, shi baya kabilanci wanda hakan ne dalilin da yasa yayi aiki don nasarar shugaba Buhari a 2015
Ministan sufuri, Chuibuke Amaechi, ya ce ya zabi kasancewa da Shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2015 maimakon Gooduck Jonathan saboda shi baya nuna kabilanci.
Tsohon gwamnan na jihar Ribas ya yi ikirarin cewa Jonathan ya gabatar masa da kawara daban-daban don ya ci gaba da kasancewa a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), amma ya ki amsa tayinsa.
Ya ce a lokacin da ya bar jam’iyyar, tsohon Shugaban kasar yayi fada da shi amma ya yi nasarar shawo kan lamarin saboda Allah na tare da shi.
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa Amaechi ya bayyana hakan ne yayinda ya tarbi wasu mambobin PDP da suka sauya sheka zuwa APC a Port Harcourt.
KU KARANTA KUMA: Ndume da sauran Sanatoci 5 da muryarsu ta fi amo a shekarar 2020
A cewar tsohon gwamnan, zai koma jihar mai albarkar man fetur a 2020 don komawa ga harkokin siyasa, sannan idan yayi hakan, zai dunga jagorantar duk wani harkoki a jihar. Ya kara da cewa duk abunda ya fadi shine zai faru.
Ya kara da bayyana cewa bai taba shan giya ba a rayuwarsa, sannan bai taba shan sigari ba kuma shi baya nuna kabilanci.
Amaechi ya kara da cewa:
“Da ina da kabilanci, shugaba Goodluck Jonathan ya gabatar mani da dama don ci gaba da kasancewa a PDP. Ya gabatar mani da duk wasu damammaki, amma na bayyana cewa nab a Buhari goyon bayana saboda ni bana kabilanci.”
KU KARANTA KUMA: Buhari ya aika wakilci mai karfi zuwa daurin auren diyar hadiminsa a Kano
A wani labarin, rikici ya barke a babban ofishin INEC, lokacin da baturen zabe, Hakeem Adikum, ya bayyana jam'iyyar APC a matsayin wacce ta samu nasarar cin zaben da aka yi ranar Asabar na Imo ta arewa.
Adikum, wanda ya mike ya sanar da yawan kuri'un da duk jam'iyyun da suka tsaya takara suka samu, yace, "Ina so in sanar da cewa APC ce ta samu nasarar cin zaben maye gurbi na Imo ta arewa, wanda aka yi a ranar Asabar, 5 ga watan Nuwamba."
Yayin sanar da sakamakon zaben, baturen zaben ya ce APC ta samu kuri'u 36,811, sai kuma Emmanuel Okewulonu na jam'iyyar PDP ya samu kuri'u 31,903.
Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng