Tirkashi: APC ta lashe kujerar sanatan Imo amma babu takamaiman dan takara

Tirkashi: APC ta lashe kujerar sanatan Imo amma babu takamaiman dan takara

- Rikici ya barke a babban ofishin INEC na jihar Imo, bayan baturen zabe ya sanar da sakamakon zaben da aka yi ranar Asabar

- Bayan Hakeem Adikum ya sanar da yadda jam'iyyar APC ta samu nasarar cin zabe a kananan hukomi 6, PDP na da karamar hukuma 1

- Mutane sun yi ta cece-kuce a kan yadda kowa ya koma gida ba tare da an sanar da wanda yayi nasarar zaben ba

Rikici ya barke a babban ofishin INEC, lokacin da baturen zabe, Hakeem Adikum, ya bayyana jam'iyyar APC a matsayin wacce ta samu nasarar cin zaben da aka yi ranar Asabar na Imo ta arewa.

Adikum, wanda ya mike ya sanar da yawan kuri'un da duk jam'iyyun da suka tsaya takara suka samu, yace, "Ina so in sanar da cewa APC ce ta samu nasarar cin zaben maye gurbi na Imo ta arewa, wanda aka yi a ranar Asabar, 5 ga watan Nuwamba."

Yayin sanar da sakamakon zaben, baturen zaben ya ce APC ta samu kuri'u 36,811, sai kuma Emmanuel Okewulonu na jam'iyyar PDP ya samu kuri'u 31,903.

KU KARANTA: Fitaccen dan kasuwa, hamshakin mai kudi kuma tsohon dan takarar shugaban kasa ya rasu

Tirkashi: APC ta lashe kujerar sanatan Imo amma babu takamaiman dan takara
Tirkashi: APC ta lashe kujerar sanatan Imo amma babu takamaiman dan takara. Hoto daga @MobilePunch
Asali: UGC

Kamar yadda Adikum yace, APC ta yi nasara a kananan hukumomi 6 da ke mazabar, sannan PDP ta yi nasara a karamar hukuma daya.

PDP ta samu nasara a karamar hukumar Obowo, karamar hukumar dan takarar. Sannan ya ce APC ta samu nasara a kananun hukumomin Okigwe, Onuimo, Isiala Mbano, Ehime Mbano da Ihitte/ Uboma.

INEC bata sanar da wani dan takara ba a matsayin mai nasara, hakan ya janyo cece-kuce a dakin taron, mabiyan 'yan takaran guda biyu, Ifeanyi Araraume da Frank Ibezim, sun yi ta cece-kuce sakamakon yadda 'yan jam'iyyar APC suke waje suna jiran a sanar da sakamako suka koma gida ba tare da an sanar ba.

Shugaban INEC na jihar Imo, Farfesa Francis Ezeonu, ya sanar da manema labarai cewa basu samu damar sanar da wanda yayi nasarar ba saboda korafe-korafe iri-iri a kan Araraume da Ibezim.

The Punch ta ruwaito yadda babbar kotun tarayya da ke Abuja ta hana Ibezim tsayawa takarar zaben a ranar Juma'a.

Sannan a ranar, kotun daukaka kara da ke Owerri ta fatattaki Araraume daga tsayawa takara a jam'iyyar APC, sannan ta tsayar da Ibezim a matsayin dan takarar jam'iyyar.

KU KARANTA: 2023: Jonathan ya yi martani a kan batun tsayawarsa takara

A wani labari na daban, Kashim Shettima, tsohon gwamnan jihar Borno, ya ce ya yi wuri shugabannin APC su fara magana a kan zaben shugaban kasa na 2023.

Ya fadi hakan ne a Ado Ekiti, babban birnin jihar Ekiti a ranar Juma'a, 4 ga watan Disamba yayin wani zaman tattaunawa na masu ruwa da tsakin jam'iyyar APC.

Kashim ya bayyana hakan, inda yace ana karkatar da hankulan shugabanni a kan abubuwan da ke faruwa a kasa a halin yanzu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: