Ndume da sauran Sanatoci 5 da muryarsu ta fi amo a shekarar 2020

Ndume da sauran Sanatoci 5 da muryarsu ta fi amo a shekarar 2020

- Shekarar 2020 ta kasance shekara mai cike da hada-hada a majalisar dattawa

- Yayinda muryoyin wasu sanatoci ya dunga amsa-kuwa a majalisar dattawan, wasu na nan amma ba a ji doriyarsu

- Wadanda muryoyinsu ya dunga amo sun tashi tsayin daka wajen kare mazabunsu da kuma bayar da gudunmawa kan lamuran da ya shafi kasa

Majalisar dattawa na dauke da mutane masu tunani da kwararru a fannoni daban-daban, kuma shakka babu tana tattare da mata da maza masu kamala a kasar.

Idan ana gudanar da muhawara a majalisar dattawa, sukan kasance yan gaba wajen bayar da gudunmawarsu, musamman kan lamura masu muhimmanci da suka shafi kasa.

Amma, duk a cikin majalisar, akwai wadanda halayyarsu ba abun koyi bane ko kadan, su dai kawai yan cikon benci ne sannan sun fi kwarewa wajen rabon ‘ganima’.

Ndume da sauran Sanatoci 5 da muryarsu ta fi amo a shekarar 2020
Ndume da sauran Sanatoci 5 da muryarsu ta fi amo a shekarar 2020 Hoto: @NGRSenate
Asali: Twitter

Abu mafi muni, shine majalisar ta fara zama wajen zaman shugabannin jiha da suka gaza wadanda ke kallon zauren a matsayin wajen zama don sunansu ya ci gaba da yawo.

A wannan shekarar ta 2020, Legit.ng ta zakulo sanatoci da suka bayar da gudunmawa, musamman wadandaa muryoyinsu yafi amo wajen bayyana ra’ayinsu, wajen kalubalantar gwamnati da kuma kafa sabbin manufa a siyasar kasar.

KU KARANTA KUMA: Buhari ya aika wakilci mai karfi zuwa daurin auren diyar hadiminsa a Kano

Ga jerin sunayen sanatocin da muryarsu ta fi amo a wannan shekarar.

1. Mohammed Ali Ndume

Sanatan mai wakiltan Borno ta kudu ya kasance daya daga cikin masu yawan fitowa a kanen labaran jaridun Najeriya a 2020.

Irin su Ndume basu da yawa. Ya kan fadi zuciyarsa koda kuwa a kan ko wanene kuma yana tsayawa mutanensa a dukkan lokaci.

2. Enyinnaya Abaribe

Shugaban marasa rinjaye a majalisar dattawa ya kasance mutum mara tsoro. A koda yaushe yana bangaren mutane kuma baya taba tsoron barazanar hukumomi.

3. Ifeanyi Ubah

Sanatan haifaffen jihar Anambra na a wa’adinsa na farko a majalisar, amma kowa ya san yana a majalisar saboda yanda gudanar da harkokinsa cikin salon a daba.

Shahararren dan kasuwa wanda ya zama dan siyasa, Ubah ya yi amfani da lokacinsa a majalisa wajen inganta lamuran mutanensa da yan Najeriya baki daya a koda yaushe.

Yan Najeriya da ke kasuwanci a Ghana wadanda ke fuskantar hukunci daga hukumomi a kasar ba za su taba mantawa da alkhairin Ubah ba kan yadda a koda yaushe yake tsayawa kan matsalolinsu.

Yan Igbo da ke kasuwanci a Lagas ma ba za su taba mantawa das hi ba kan yadda yake nemansu da magance masu matsalolinsu.

KU KARANTA KUMA: Kasar Amurka ta yafewa ƴan Najeriya kuɗin Biza

4. Sani Mohammed Musa

Yana wakiltan Niger ta gabas a majalisar tarayyar. Ya hau wannan matsayi a lokacin da mazabarsa ke fuskantar yawan hare-hare daga yan bindiga.

Sanata Musa ya kasance mai fadin gaskiya game da lamura a majalisar dattawan. Kusan ko wani mako sai sanatan ya tashi a zauren majalisa domin janyo hankalin takwarorinsa kan ta’asar da yan bindiga ke yi a yankinsa.

5. Smart Adeyemi

Kasancewarsa dan jarida kuma mai rajjin kare hankin dan adam ya sa ya zama mai yawan surutu. Amma abunda zai burge ka game da kasancewar Adeyemi cikin wannan rukunin shine cewa ya shiga zauren majalisa yan watanni da suka gabata bayan ya sha gwagwarmaya tare da yin nasara kan abokin adawarsa.

Adeyemi ya sa an san da kasancewarsa a wajen. Cikin yan watannin, yana daga muryarsa sosai game da matsalolin kasar. A matsayinsa na Shugaban kwamitin majalisa kan sufurin sama, sanatan na ta gano wasu matsaloli sannan yana ta kira ga gwamnati kan ta dauki mataki a kansu ba tare da bata lokaci ba.

6. Elisha Abbo

Ya kasance sanata mafi karancin shekaru a majalisar amma a koda yaushe baya bari a barsa a baya wajen fadin ra’ayinsa.

Abbo wanda ya kasance dan siyasa daga jihar Adamawa ya tashi tsayin daka domin nunawa duniya cewa ya cancanci wakiltan mutanensa duk da rigingimun da ke kewaye da shi.

A lokacin da yan ta’adda suka far ma mazabarsa, Abbo ya tashi tsayee a majalisar inda ya caccaki hukumomin tsaro da gwamnati. Ya yi magana cike da damuwa sannan yayi kira ga gyara tsarin tsaron Najeriya.

Tun daga lokacin, matashin sanatan ya zamo mai daga muryarsa da bayar da gudunmawa a muhawara a zauren majalisar.

A wani labarin, an alanta dan takaran jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a zaben kujeran Sanata mai wakiltan mazabar Legas ta gabas, Tokunbo Abiru, matsayin wanda ya lashe zaben.

A bisa alkaluman da hukumar gudanar da zabe ta kasa mai zaman kanta, INEC, ta sanar, Tokunbo Abiru ya samu jimillan kuri'u 89,204, yayinda Babatunde Gbadamosi, na Peoples Democratic Party (PDP) ya samu kuri'u 11,257.

Abiru ya lallasa abokin hamayyarsa na tazara mai fadin gaske a dukkan kananan hukumomin, The Nation ta ruwaito.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng