Buhari ya aika wakilci mai karfi zuwa daurin auren diyar hadiminsa a Kano
- Shugaba Muhammadu Buhari ya aika wata tawaga ta musamman zuwa daurin auren diyar hadiminsa
- Buhari ya shawarci ma'auratan da su zamo masu yarda da mutunta juna a gidan aurensu
- Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ne ya bayar da auren yarinyar babban dogarin shugaban kasar
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aika wata tawaga karkashin jagorancin ministan tsaro, Manjo Janar Bashir Salihi Magashi mai ritaya, zuwa wajen bikin yarinyar babban dogarinsa, Amina Idris Ahmed da angonta, Hayatuddeen Mustapha Abba.
Shugaba Buhari, a sakonsa, ya shawarci sabbin ma’auratan a kan su gina ginshikin aurensu bisa yarda da mutunta juna.
Shugaban kasar, a cikin wata sanarwa da kakinsa, Garba Shehu ya saki, ya bukaci ma’auratan da “kowanne ya kula da dan uwansa kamar yadda yake so a kula da shi” sannan ya yi masu fatan nasara a gidan aurensu.
KU KARANTA KUMA: Kaothar Ajani: Marainiya mai shekaru 16 da ke tukin Napep don ciyar da kanninta
Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, shine ya mika auren amaryar, jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Tawagar sun hada da ministan ruwa kuma Galadiman Kazaure, Injiniya Suleiman Adamu, babban mai ba Shugaban kasa shawara a kan harkokin cikin gida, Sarki Abba.
Sai babban mai ba Shugaban kasa shawara kan harkokin lamarai, Garba Shehu; Ambasada Lawal Kazaure, hadimi na musamman a ofishin Shugaban kasa, Sabi’u Tunde Yusuf.
Sauran sune jami’in tsaro na musamman ga Shugaban kasa, DCP Aliyu Abubakar Musa; Sakataren dindindin; maalisar jiha, Tijjani Umar; da kuma mai ba karamin ministan albarkatun man fetur shawara, Injiniya Nuhu Dauda.
KU KARANTA KUMA: 2023: Jigo a APC ya bayyana mutanen da za su fitar da yankin shugaban kasa
A wani labarin, wata matashiya yar Najeriya mai suna @Hafsaat_mohd a shafin Twitter ta wallafa hotunanta sanye da hijabi a yanar gizo, inda ta tambayi mutane ko tayi kama da mawakiyar Amurka Nicki Minaj.
Yayinda wasu suka yaba da kyawunta, wasu sun je karkashin hotunanta domin caccakar kwantancin da tayi, cewa mace mai mutunci ba za ta hada kanta da mutum da baida mutunci ba.
Akwai kuma wasu da suka ce ta fi mawakiyar kyau. Hotunan nata ya tattara dubban sharhi daga mutane.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng