Yanzu-yanzu: Jam'iyyar APC ta lashe zaben kujeran Sanata Legas ta gabas

Yanzu-yanzu: Jam'iyyar APC ta lashe zaben kujeran Sanata Legas ta gabas

An alanta dan takaran jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a zaben kujeran Sanata mai wakiltan mazabar Legas ta gabas, Tokunbo Abiru, matsayin wanda ya lashe zaben.

A bisa alkaluman da hukumar gudanar da zabe ta kasa mai zaman kanta, INEC, ta sanar, Tokunbo Abiru ya samu jimillan kuri'u 89,204, yayinda Babatunde Gbadamosi, na Peoples Democratic Party (PDP) ya samu kuri'u 11,257.

Abiru ya lallasa abokin hamayyarsa na tazara mai fadin gaske a dukkan kananan hukumomin, The Nation ta ruwaito.

Ga sakamakon kananan hukumomin:

Shomolu

APC: 17,728

PDP: 2,067

Epe

APC: 22,213

PDP: 1,826

Ibeju Lekki

APC: 16,336

PDP: 937

Ikorodu

APC: 19,204

PDP: 3,766

Kosofe

APC: 13,723

PDP: 2,661

Yanzu-yanzu: Jam'iyyar APC ta lashe zaben kujeran Sanata Legas ta gabas
Yanzu-yanzu: Jam'iyyar APC ta lashe zaben kujeran Sanata Legas ta gabas
Source: UGC

Source: Legit

Online view pixel