Kasar Amurka ta yafewa ƴan Najeriya kuɗin Biza

Kasar Amurka ta yafewa ƴan Najeriya kuɗin Biza

- Gwamnatin Amurka ta yafe biyan kudin biza ga 'yan Nigeria ma su sha'awar ziyartar kasar

- Ma'aikatar harkokin waje ta Amurka ta ce cire kudin ya biyo bayan ragi da cire kudin daukan hoton zanen yatsa da FG ta yi wa Amurkawa ma su son zuwa Nigeria

- A cewar ma'aikatar, ma su sha'awar ziyartar kasar Amurka za su iya ziyartar shafin yanar gizo www.travel.state.gov domin karin bayani

Gwamnatin ƙasar Amurka ta sauke nauyin biyan kuɗin biza ga dukkan ƴan ƙasar Najeriya kuma tsarin zai fara aiki daga ranar 3 ga watan Disamba 2020, kamar yadda jaridar Vanguard ta wallafa ranar Asabar.

Kamar yadda bayanai suka nuna daga ma'aikatar harkokin kasashen waje ta Amurka, ta cikin wata sanarwa da kakakinta, Ferdinand Nwonye, ya fitar ranar Asabar, ta yi bayani kamar haka;

"Ma'aikatar harkokin waje na sanar da cewa gwamnatin ƙasar Amurka ta cire kuɗaɗen biza ga ƴan Najeriya masu buƙatar bizar ƙasar Amurka.

KARANTA: PDP ce kan gaba yayin da INEC ta ce zaben maye gurbi a Zamfara 'bai kammalu ba' bayan bacewar ma'aikata biyu

"Wannan cigaba ya zo ne a matsayin godiya bisa tsarin rage adadin yawan kudin biza da kuma kuɗin ɗaukar zanen yatsu da ƴan ƙasar Amurka masu buƙatar bizar Najeriya ke biya wanda gwamnatin Najeriya ta yi."

Kasar Amurka ta yafewa ƴan Najeriya kuɗin Biza
Kasar Amurka ta yafewa ƴan Najeriya kuɗin Biza
Asali: UGC

"Saboda haka, gwamnatin ƙasar Amurka ta soke kuɗaɗen bizar shigowa ƙasar Amurka ga ƴan Najeriya daga ranar 2 ga watan Disamba."

"Ga duk Ƴan Najeriya masu buƙatar tafiya ƙasar Amurka, ana shawartar su da su ziyarci adireshin yanar gizo www.travel.state.gov don samun ƙarin bayanai," a cewar sanarwa da hukumar ta wallafa.

KARANTA: Kamfanin sufurin jiragen sama na Arik sun sallami ma'aikatansu 300 rigis

A wani labarin da Legit.ng Hausa ta wallafa, shugaba Buhari ya bayar da umarnin sakin sabbin manyan motocin alfarma domin saukakawa jama'a kalubalen sufuri da rage musu radadin kara farashin man fetur.

Buhari ya mika sakon godiyarsa ga 'yan Najeriya bisa abin da ya kira 'hakurin da suka nuna' dangane da kalubalen tattalin arziki da kasa ke fuskanta

Kazalika, ya godewa mambobin kungiyar kwadago bisa fahimta da dattakon da kuma kishin kasa da suka nuna.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel