Matashiya sanye da hijabi ta wallafa hotunanta, ta nemi sanin ko da gaske tana kama da Nicki Minaj

Matashiya sanye da hijabi ta wallafa hotunanta, ta nemi sanin ko da gaske tana kama da Nicki Minaj

- Ana ta cece-kuce kan hotunan wata matashiya sanye da hijabi wacce ta wallafa hotunanta a kan Twitter, tana tambayar ko tana kama da Nicki Minaj

- Mutane da dama na kallon hakan a matsayin cin mutuncin addininta tunda har za ta iya yin wannan kwatanci da mawakiyar ta Amurka

- Akwai kuma mutanen da suka kasa gane abunda ya fusata mutane game da matashiyar wacce ta wallafa kyawawan hotunanta a yanar gizo

Wata matashiya yar Najeriya mai suna @Hafsaat_mohd a shafin Twitter ta wallafa hotunanta sanye da hijabi a yanar gizo, inda ta tambayi mutane ko tayi kama da mawakiyar Amurka Nicki Minaj.

Yayinda wasu suka yaba da kyawunta, wasu sun je karkashin hotunanta domin caccakar kwantancin da tayi, cewa mace mai mutunci ba za ta hada kanta da mutum da baida mutunci ba.

Akwai kuma wasu da suka ce ta fi mawakiyar kyau. Hotunan nata ya tattara dubban sharhi daga mutane.

Matashiya sanye da hijabi ta wallafa hotunanta, ta nemi sanin ko da gaske tana kama da Nicki Minaj
Matashiya sanye da hijabi ta wallafa hotunanta, ta nemi sanin ko da gaske tana kama da Nicki Minaj Hoto: @Hafsaat_mohd
Source: Instagram

KU KARANTA KUMA: Lai Mohammed ya ce sai Buhari ya kammala wa’adinsa duk da kira da ake yi na yayi murabus

Kalli wallafar tata a kasa:

Ga wasu daga cikin sharhin:

@al_muhammadu yace:

“Ina sa ran za ki fusata idan wani ya fada maki cewa kina kama da Nicki Minaj, a wajena hakan cin mutunci ne sosai gaskiya kada ki kwatanta kanki da irin wannan matar.”

@Farouqaadam1 yace:

"Subhanal_Lah, baki yi kama da ita ba. Dan Allah ki yi watsi da wannan Kalmar, ke Musulma ce, kin fita sosai; kamar tazarar da ke tsakanin sammai da kassai.”

@goodconstantine ya ce:

"Zancen gaskiya. Ki so ki yi kama da ita. Ina son Nicki amma an yi aiki sosai kafin ta kai yadda take a yau.”

@Red_negro_ yace:

"Lmao. Na bude fagen sharhi don yabawa da kyawun yarinyar nan kawai sai naga mutane suna nuna kiyayya kan matar da ta fi ahlinsu gaba daya.”

@MosesRhyris tace:

"Dukkanin mutanen nan da ke cewa kada ta kwatanta kanta da ita za ka same su da wakokin Nicki Minaj dankare a wayoyinsu...munafirci.”

KU KARANTA KUMA: Hotunan kamun auren jarumin Kannywood, Nuhu Abdullahi

A gefe guda, an gano bidiyon wata amarya da angonta kwanan nan a shafin soshiyal midiya kuma ya samu martani na ban dariya daga yan Najeriya.

Bidiyon ya nuno wasu ma’aurata a wajen liyafar aurensu. Da aka kai lokacin ciyar da ango sai aka gano sabuwar amaryar ta tsuguna kan gwiwowinta yayinda shi kuma angon ya zauna kan wani kayataccen kujera fari.

Kyakyawar amaryar, wacce ke sanye da kaya launin ja, ta dibi abinci a hannunta don ciyar da angonta.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel