Kaothar Ajani: Marainiya mai shekaru 16 da ke tukin Napep don ciyar da kanninta

Kaothar Ajani: Marainiya mai shekaru 16 da ke tukin Napep don ciyar da kanninta

- Wata yarinya mai shekaru 16 ta fara sana'ar tukin Napep a jihar Osun

- Kaothar ta fara sana'ar ne bayan mutuwar mahaifinta wanda ya siya Napep din a bashi

- Tana taimakon kanninta da mahaifiyarta, sannan tana karasa biyan kudin Napep har N750,000

Wata yarinya ta koma sana'ar tukin Keke-Napep don kulawa da kanninta da kuma biyan basukan da ake bin mahaifnta da ya mutu.

Wata Kaothar Ajani, mai shekaru 16, ta zage wurin sana'ar tukin Keke-Napep bayan mutuwar mahaifinta. Tana sana'ar ne don kulawa da kanta da mahaifiyarta.

A al'adar Afirika, akwai ayyuka daban-daban wadanda aka saba maza ne suke yi, ba haramun ne mata su yi ba, amma kuma maza ne suka yi fice a sana'o'in.

Kaothar Ajani: Marainiya mai shekaru 16 da ke tukin Napep don ciyar da kanninta
Kaothar Ajani: Marainiya mai shekaru 16 da ke tukin Napep don ciyar da kanninta
Source: Original

Ana ganin mata a mutane masu rauni, ba za su iya kujuba-kujuba ba kamar maza. Ayyukan karfi da wadanda suke bukatar tsawon lokaci sun fi kyau ta maza.

Kaothar Ajani tana kulawa da 'yan uwanta ta sana'ar tukin Napep. Labarin Kaothar na daban ne, don mafi yawan mutane suna kallon abun wani iri, saboda karfin hali irin na yarinyar.

KU KARANTA: Fitaccen dan kasuwa, hamshakin mai kudi kuma tsohon dan takarar shugaban kasa ya rasu

Yarinyar wacce ta sanar da wakilin Legit.ng na jihar Osun, Gboyega Bakare, cewa tana aji 5 na sakandare labarin yadda take tafiyar da rayuwarta ta sana'ar Napep.

Da aka tambayeta dalilinta na zabar sana'ar da kowa yasan maza ne suke yin ta, cewa tayi sana'ar ce ta zabe ta ba tare da ta samu wani zabi ba.

A cewarta, mahaifinta ya siya Napep din watanni 7 da suka wuce a N750,000, kafin ya fara ciwo ya mutu.

A matsayina na babbar diyarsa, kuma ina da kanni masu bukatar taimakona, sai na fara sana'ar tukin Napep don in tallafa wa 'yan uwana kuma in biya ragowar bashin da ake bin mahaifina na kudin Napep din.

Kaothar ta ce tana da burin zama ma'aikaciyar jinya a rayuwarta. Ta ce lokacin da ta fara sana'ar, ta wahala kwarai.

KU KARANTA: Zaben maye gurbi: 'Yan bindiga sun tarwatsa masu kada kuri'a a Zamfara

A cewarta, da farko mahaifiyarta ba ta amince da sana'ar ba, ta gwammace wanda yake bin mahaifinta bashi ya dauki Napep dinsa, amma daga baya ta amince.

A cewar yarinyar, da farko tana wahala, saboda idan ta koma gida daga makaranta, sai ta shirya ta tafi sana'a. Amma daga baya ta saba.

A cewarta mahaifinta ya tasheta kamar namiji, shiyasa har ta samu karfi da kwarin guiwa wurin yin aikin bayan mutuwarsa.

Ta ce idan ta fara tukin Napep tun karfe 3 zuwa 7 na yamma, tana samun N5000 a kowacce rana, amma a ranakun da bata samu kudi sosai ba, tana samun N2000.

Ranakun karshen mako kuma tana samun N10,000. Amma ta ce tana gudun daukar fasinjoji masu kayan nauyi, wani lokacin kuma wasu maza suna taya ta lodin kayan cikin Napep din.

Tace tana da burin zama ma'aikaciyar jinya, amma bata san me Ubangiji zai yi ba nan gaba.

A wani labari na daban, Ishaku Elisha Abbo, Sanata mai wakiltar mazabar Adamawa ta arewa ya tsallake rijiya da baya.

Kamar yadda Legit.ng ta ga wata takarda wacce tazo daga ofishin yada labaran sanatan, wani mutum mai dauke da bindigar toka ya lallabo ya tare shi, inda yayi barazanar harbinsa matsawar bai bashi miliyan 2 ba.

Takardar, wacce hadimin sanatan a kan harkokin yada labarai, Michael Volgent ya saka hannu, ya ce al'amarin ya faru ne da misalin 2pm, inda matasa da yawa suka tare hanyar, yana hanyarsa ta zuwa bikin dan uwansa da ke Mubi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel