Alaafin: Ina so in amfana da shawarar manya inji Aminu Ado-Bayero

Alaafin: Ina so in amfana da shawarar manya inji Aminu Ado-Bayero

-Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero ya kai wa Sarkin kasar Oyo ziyara

-Aminu Bayero yace akwai bukatar ya samu albarkar Mai martaba Alaafin

-Tun ba yau, akwai kyakkyawar alaka tsakanin Masarautar Oyo da ta Kano

Mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado-Bayero, ya yaba da basirar Alaafin na kasar Oyo, Oba Lamidi Adeyemi wajen kokarin rike kasar nan.

Punch ta rahoto cewa Sarki Aminu Ado Bayero ya bayyana wannan a ranar Alhamis, 3 ga watan Disamba, 2020, lokacin da ya kai masa ziyara.

Jaridar ta ce Sarkin na Kano ya bayyana cewa a shirya yake ya dauki darasi da shawarar manya daga wurin dattijon Basaraken mai shekara 82.

“Alfarma ce da muka samu damar ziyarar Alaafin da mu ka zo kasar Kudu maso yamma a karo na biyu tun da mu ka hau gadon mulkin iyayenmu.”

KU KARANTA: Tsohon Sarki Sanusi II ya koma karatu bayan barin mulki

Mai martaba Aminu Ado Bayero ya ce: “Mun zo Oyo domin a cigaba da rike dangantakar da marigayi mahaifi na ya tsira, ya kuma raya ta.”

“Mun zo mu samu albarkaci da basirar Mai martaba.” Sarkin na Kano ya ce sun zo kasar Oyo ne domin nuna cewa kasashen biyu ‘yanuwan juna ne.

Bayero wanda ya hau mulki a bana ya ce: “Tarihin Oyo kamar Kano ne, suna nan tun daruruwan shekaru kafin kafuwar abin da ake cewa Najeriya yau.”

Alhaji Aminu Ado Bayero ya ce tun can Kano da Oyo sun yi kaurin-suna a harkar kasuwanci da sha’anin shugabanci, da kuma kwarewa a fannin tsaro.

KU KARANTA: Sarkin Zazzau ya fashe da kuka ya na tsakar jawabi?

Alaafin: Ina so in amfana da shawarar manya inji Aminu Ado-Bayero
Alhaji Aminu Ado Bayero Hoto: pmnewsnigeria.com
Source: UGC

Alaafin ya bada labarin yadda shi da Ayo Bayero su kayi kokarin ganin ana ba masarautu 5% na kason abin da ke shiga hannun kananan hukumomi.

A kasar Zazzau kuma, kun ji cewa an dakatar da Wazirin Zazzau, Alhaji Ibrahim Aminu, hakan na zuwa ne bayan an aika masa da takardar tuhuma.

Rahotanni sun ce ana zargin Ibrahim Aminu da laifin rashin halartan wani taron da ma'aikatar kananan hukumomin jihar ta shirya a jihar Kaduna.

A halin yanzu Iyan Zazzau ya shigar kara kotu ya na kalubalantar nadin Ahmad Nuhu Bamalli.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit Nigeria

Online view pixel