Gwamnatin jihar Kaduna ta dakatad da shugaban kwamitin zaben sarki, Wazirin Zazzau

Gwamnatin jihar Kaduna ta dakatad da shugaban kwamitin zaben sarki, Wazirin Zazzau

- Bayan aike masa da takardar tuhuma, an dakatad da Wazirin Zazzau

- Ana zarginsa da rashin halartan taron da ma'aikatar kananan hukumomin jihar ta shirya

- Iyan Zazzau, Aminu Idris ya shigar kara kotu inda yake kalubalantar nadin Bamalli matsayin sarki

Gwamnatin jihar Kaduna ta dakatad da shugaban kwamitin masu zaben sarkin Zazzau, Wazirin Zazzau, Alhaji Ibrahim Aminu, Sahara Reporters ta ruwaito.

Hakazalika ta gargadi Iyan Zazzau, Aminu da sauran mambobin kwamitin zaben sarkin uku su canza lauyansu zuwa lauyan gwamnati a karar da suka shigar kotu, kan nadin Ahmed Nuhu Bamalli a matsayin sabon Sarkin Zazzau.

Za ku tuna cewa Iyan Zazzau, ya shigar da kara kotu inda ya ke kalubalantar nadin Ahmad Bamalli matsayin sabon sarkin masarautar.

Gwamnatin jihar, a wasikar da sakataren din-din-din na ma'aikatar harkokin kananan hukumomi ya rattafa hannu a madadin kwamishanan, ta sanar da dakatad da Wazirin Zazzau.

"Mun fahimci cewa sabon sarkin da gwamnatin jihar sun yiwa masu zaben sarki barazanar su canza lauyansu zuwa lauyan jihar, saboda su rattafa hannu kan jawabin rantsuwa," wata majiya ta bayyanawa Sahara Reporters.

"Barazanar da Sarki da gwamnatin jihar keyi ne ya sa aka aika wasikar tuhumar ranar 12 ga Nuwamba, 2020."

"Kawo yanzu dai, daya daga cikin masu zaben sarkin ya amince da canza lauyansa zuwa na gwamnati."

KU KARANTA: Dogarin kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, ya bindige mai jarida ba gaira, ba dalili

Gwamnatin jihar Kaduna ta dakatad da shugaban kwamitin zaben sarki, Wazirin Zazzau
Gwamnatin jihar Kaduna ta dakatad da shugaban kwamitin zaben sarki, Wazirin Zazzau Hoto: Newnigeriannewspaper
Asali: UGC

KU DUBA: Najeriya za ta fara shigo da man fetir daga kasar Nijar, an yi yarjejeniya

Mu kawo muku cewa an aikewa 'yan majalisar sarki takardar tuhuma mai taken "rashin halartar taron tattaunawa da ma'aikatar kananan hukumomi ta shirya"

Daga cikin wandanda aka aikewa takardar akwai limamin Zazzau, Wazirin Zazzau, Limamin Kona da Makama Karami kan rashin halartar wani taro da aka yi kan shirin bikin mika sandar sarauta ga sabon sarkin Zazzau.

An bada awa 48 ga wanda suka karbi tuhumar da suyi bayani, sai dai wani rahoto ya nuna wasu daga cikin masu zaben sarkin, basa jin dadin yadda al'amura ke gudana a masarautar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng