Tsohin Sarkin Kano, Sanusi Lamido, zai koma makaranta

Tsohin Sarkin Kano, Sanusi Lamido, zai koma makaranta

- Tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya sake samun gurbin aiki a jami'a

- Sanusi ya samu gurbin hadaka da shararriyar jami'ar Oxford dake kasar Ingila

- A cewar jami'ar, Sanusi zai yi rubutawa jami'ar wani littafi kan tattalin arzikin Najeriya

Tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na biyu, ya koma makaranta yayinda shararriyar jami'ar Oxford dake kasar Birtaniya ta bashi gurbin aiki da karatu.

Kwamitin lamuran nahiyar Afrika a jami'ar ta sanar da hakan bayan amsa bukatar da tsohon sarkin ya gabatar.

Sanusi zai koma makarantan a watan Oktoba kuma zai yi amfani da lokacin wajen rubuta wani littafi bisa abubuwan da ya fuskanta a matsayin ma'aikacin banki, mai sharhi kan lauran yau da kullum, masanin tattalin arziki kuma tsohon gwamnan babban bankin Najeriya CBN.

A cewar jami'ar Oxford, Sanusi wanda ya shugabanci bankin CBN daga 2009 zuwa 2014 "zai yi amfani da lokacin hadakan domin rubuta wani littafi mai taken: "Matakin da bankin CBN ta dauka kan matsin tattalin arziki a duniya: Dubi na musamman cikin babban bankin Najeriya ."

Tsohin Sarkin Kano, Sanusi Lamido, zai koma makaranta
Tsohin Sarkin Kano, Sanusi Lamido, zai koma makaranta
Asali: UGC

KU KARANTA: Rikicin majalisar jihar Kaduna ya dau sabon salo: An dakatad da yan majalisa 3, an zajjara 5

Jami'ar Oxford na daya daga cikin manyan jami'o'in duniya dake gudanar da karatu kan nahiyar Afrika.

Shahrarren masanin tattalin arziki, Sanusi, ya rasa mulkinsa lokacin gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya kwance masa rawani kan laifin rashin biyayya da almundahana.

Tuni ya koma gidansa dake jihar Legas da zama bayan kotu ta hana ajiyeshi a Nasarawa.

Za ku tuna cewa, Legit.ng ta ruwaito gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i, ya nada tsohon sarkin matsayin Cansalan jami'ar Kaduna, KASU.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel