Dalilin fashewar Sarkin Zazzau da kuka yayin gabatar da jawabin nada shi

Dalilin fashewar Sarkin Zazzau da kuka yayin gabatar da jawabin nada shi

- An gudanar da bikin nadin sabon sarkin Zazzau, Ahmad Nuhu Bamalli, a ranar Litinin, 9 ga watan Nuwamba

- Bisa al'ada gwamnati kan gudanar da bikin mika sandar iko ga kowanne babban sarki bayan nada shi

- Mai martaba Ahmad Nuhu Balli ya zama sarkin masarautar Zazzau bayan mutuwar tsohon sarki, Shehu Idris, ranar 20 ga watan Satumba

A ranar Litinin, 9 ga watan Nuwamba, ne aka yi bikin mika sandar iko ga sabon sarkin masarautar Zazzau, Ahmad Nuhu Bamalli.

Taron bikin ya samu halarta manyan sarakunan arewa da sauran masu rike da mukamai na gwamnati da na siyasa musamman 'yan asalin arewacin Najeriya.

A yayin da ya ke gabatar da jawabinsa, Mai martaba Ahmad Nuhu Bamalli, ya fashe da kuka a daidai lokacin da ya ke mika godiya ga Allah da gwamnatin jihar Kaduna.

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa'i, ne ya mika sandar iko ga Mai martaba Ahmad Nuhu Bamalli yayin taron.

KARANTA: 'Yan bindiga sun kai hari ofishin 'yan sanda, sun kashe jami'ai biyu, sun yashe ma'adanar makamai

Kukan Sarkin na Zazzau ya zo ne a daidai lokacin da ya ke fadin; "ina godiya ga Allah da gwamnatin jihar Kaduna a kan wannan nadi da aka yi min a matsayin Sarkin masarautar Zazzau na goma sha tara (19).

Dalilin fashewar Sarkin Zazzau da kuka yayin gabatar da jawabin nada shi
Sarkin Zazzau a wurin bikin nada shi @masarautar_zazzau
Asali: Twitter

"Na gaji sarauta ne daga Kakana Malam Musa wanda ya fito daga tsatson 'Mallawa', shi kuma Usman Danfodio ne ya bashi tuta," a cewarsa.

DUBA WANNAN: Kaduna: An sake tsintar gawar matasan 'yammata biyu a Kurmin Mashi a karo na uku

Mai martaba Ahmad Nuhu Bammalli ya zama sarkin masarautar Zazzau na 19 bayan mutuwar tsohon sarki, Shehu Idris, a cikin watan Satumba.

Legit.ng Hausa ta wallafa cewa bayan sanar da sabon Sarkin Zazzau da Gwamna Nasir El-Rufai ya yi a ranar 9 ga watan Nuwamba, ya mika masa sandar sarautar kasar Zazzau a ranar Litinin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel