DHQ ta maida martani ga NGF, ta ce yakin Boko Haram bai fi karfinta ba

DHQ ta maida martani ga NGF, ta ce yakin Boko Haram bai fi karfinta ba

- Hedikwatar tsaro ta musanya maganar da kungiyar NGF tayi a makon nan

- Shugaban gwamnoni Kayode Fayemi, yana ganin aiki ya fi karfin sojojinmu

- John Enenche yace ba haka abin yake ba, ya kuma yi magana kan sojin gona

Mun samu labari daga Daily Trust cewa Hedikwatar tsaron Najeriya ta soki jawabin da ya fito daga bakin shugaban gwamnonin Najeriya, Kayode Fayemi.

Sojojin kasar sun musanya maganar da kungiyar gwamnoni watau NGF ta yi na cewa aiki ya yi wa jami’an sojoji yawa, hedikwatar tsaron ta ce ba haka ba ne.

Wajen tattauna wa da ‘yan jarida a birnin tarayya Abuja a ranar 3 ga watan Disamba, Manjo Janar John Enenche, ya yi magana a kan dauko hayar sojojin waje.

KU KARANTA: Rashin tsaro: Sule Lamido ya ce Buhari ya tashi ya nemi gafarar Allah

Janar John Enenche ya ce gwamnatin tarayya ce kawai ta ke da ikon dauko wasu sojoji daga ketare domin su taimaka wa Najeriya wajen yakar ‘yan ta'adda.

Ya ce “Iyayen gidanmu da su ka daukemu sun ce aiki ya yi mana yawa, ya rage nasu. Ba aikin soji ba ne suce aiki ya yi masu yawa; Ni aiki bai yi mani yawa ba.”

“Idan nace haka, ina nufin bana son in yi aiki. Kuma idan na ce ba haka ba ne, ina nufin ba a amfani da karfina kenan.” inji Janar din a madadin gidan sojan.

Janar Enenche ya ce: “Maganar dauko kwararru daga ketare ta fi karfinmu. Irin dakarun da ake da su ya danganta ne da mutane, wannan ya zarce karfin ikonmu.”

KU KARANTA: Shehu Sani ya soki maganar da Janar Buratai

DHQ ta maida martani ga NGF, ta ce yakin Boko Haram bai fi karfinta ba
DHQ Hoto: dailytrust.com
Source: UGC

DHQ tace wannan magana ba huruminta ba ne. “Babu sojojin da suke fada wa mutane cewa ga yadda muke so muyi aiki. Aikin ‘yan majalisa da majalisar tsaro ne.”

A gefe guda kuma kun ji cewa babban malamin addinin musuluncin nan, Ahmad Abubakar Gumi, yace rikicin kudancin Kaduna ya dauki tsawon lokaci ana fama.

Dr. Ahmad Abubakar Gumi yace ya zama tilas mutanen kirki, maza da mata, su hada karfi da karfe wurin kawo karshen wannan tsohon mummunan rikicin addini.

Kafin yanzu, Ahmad Abubakar Gumi ya fito ya na neman shugaba Muhammadu Buhari ya yi murabus.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit Nigeria

Online view pixel