Shehu Sani ya yi wa Buratai 'wankin babban bargo' a kan wa'adin da ya bai wa Boko Haram

Shehu Sani ya yi wa Buratai 'wankin babban bargo' a kan wa'adin da ya bai wa Boko Haram

- Tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya, ya caccaki shugaban rundunar sojin kasa a kan wasu kalaman da ya furta

- Ya yi wannan caccakar ne a shafinsa na Twitter, a ranar Alhamis, inda yace basirar Buratai ta kare alamu ne na yana bukatar murabus

- Buratai ya ce ta'addanci zai iya cigaba da wanzuwa har nan da shekaru 20 masu zuwa, wadannan ne suka fusata sanatan

Tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani, a ranar Alhamis, ya caccaki shugaban rundunar sojin kasa, Lt. Janar Tukur Buratai, a kan yadda yace ta'addanci zai iya cigaba da wanzuwa har nan da shekaru 20 a Najeriya.

The Punch ta ruwaito yadda shugaban sojin kasa yayi wata magana bayan 'yan kwanaki da 'yan Boko Haram suka kashe manoman shinkafa 43 a jihar Borno.

Tsohon sanatan ya mayar da martani a kan maganar, ta shafinsa na kafar sada zumuntar zamani ta Twitter a ranar Alhamis, inda yace kalaman Buratai suna nuna karewar basira da rashin dabarun yaki.

Shehu Sani ya yi wa Buratai 'wankin babban bargo' a kan wa'adin da ya bai wa Boko Haram
Shehu Sani ya yi wa Buratai 'wankin babban bargo' a kan wa'adin da ya bai wa Boko Haram. Hoto daga @MobilePunch
Asali: Twitter

KU KARANTA: Budurwar da ke samun kudin da bai ka N50,000 ba tana tamfatsa katon gida, ta janyo cece-kuce

Kamar yadda Shehu Sani ya wallafa, "Sanar da mutanenmu cewa tabarbarewar harkokin tsaro za su cigaba har na tsawon shekaru 20 alamace da ke nuna gazawa da karewar basirarka a matsayinka na soja.

"Kuma alama ce wacce take nuna kana bukatar murabus, sannan kuma kana nuna wa duniya alamar cire rai daga samun nasara ne."

KU KARANTA: Obasanjo: Dalilin da yasa na hana Gani Adams kawo min ziyara

A wani labari na daban, babban malamin addinin musulunci na jihar Kaduna, Dr Ahmad Abubakar Gumi, ya ce rikicin kudancin Kaduna ya dauki lokaci mai tsawo, Daily Trust ta wallafa.

A cewarsa, ya zama tilas mutanen kirki, maza da mata, su hada karfi da karfe wurin kawo karshen rikicin addinin.

Dr Gumi, wanda shine shugaban KHF ya fara shirin kawo karshen rikicin addini da ke addabar kudancin Kaduna, wanda yake hana cigaba da zaman lafiya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: