“Makwaidatan Malamai, Barayin ‘Yan siyasa da kuma Matsorata aka tara a Arewa”

“Makwaidatan Malamai, Barayin ‘Yan siyasa da kuma Matsorata aka tara a Arewa”

- Naja’atu Mohammed tace an tara munafukai, matsorata, barayi a Yankin Arewa

- ‘Yar siyasar tace ta sare da Gwamnatin Buhari duk da irin bautar da su kayi mata

- Naja’atu Mohammed da Sule Lamido sun bada shawara mutane su koma wa Allah

Jaridar BBC Hausa tayi hira da tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamido, inda aka ji ta bakinsa game da rawar ganin wannan gwamnati ta Muhammadu Buhari.

Alhaji Sule Lamido ya ce akwai bukatar shugaban kasar ya yi addu’a, ya kuma nemi gafarar Allah.

“Shi ya kamata ya kalli kansa, ya ce shin me ya yi wa Allah, ya tashi cikin dare, ya yi sallah raka’a biyu, ya sa goshinsa a kasa, ya yi kuka.” Inji Sule Lamido.

‘Dan adawar ya ce: “Abubuwa da yawa da (Buhari) ya fada kafin ya hau mulki, ya gaza; tsaro, tattalin arziki, da sauransu. Watakila sai ya tashi ya ce: “Allah na tuba.”

KU KARANTA: Sojoji sun yi wa Boko Haram sabon tanadi

Game da abin da mutanen kasa za suyi, tsohon gwamnan na PDP ya ce: ”‘Yan Najeriya suna addu’a, lokacin da Buhari bai da lafiya, sun yi masa addu’a.”

Lamido wanda ya rike Ministan harkar waje a baya, ya ce idan har shugaban kasar ya na yin addu’a, za a shawo kan matsalolin rashin tsaro da ake fama da shi.

Ita ma Naja’atu Mohammed ta yi hira da RFI Hausa, ta ce gwamnati ta gaza kare rai da dukiyar ‘yan kasa. “Wannan gwamnati ba ta amfani kasa da komai ba.”

Hajiya Naja’atu tace mafi yawan mutanen Arewa munafukai ne, shirun manya da malaman yankin yasa ake cigaba da kashe jama’a, amma ba ayi komai ba.

KU KARANTA: Kashe-kashe ya sa mu cikin hadarin rashin isasshen abinci

“Makwaidatan Malamai, Barayin ‘Yan siyasa da kuma Matsorata aka tara a Arewa”
Naja’atu Mohammed ta hakura da Gwamnatin Buhari Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

“Gwamnatin Buhari ba ta tausayin al’umma, musamman ‘Yan Arewa. Da Buhari ya damu, da ya yi tankade da rairaye.” Naja’atu ta yi kira a koma wa Ubangiji.

‘Yar gwagwarmayar ta ce ta sare da tafiyar gwamnatin APC domin ba a taba satar dukiyar kasa kamar a wannan gwamnati ba, sannan an rasa dinbin rayuka.

Dazu kun ji tsohon Gwamnan Jihar Borno, Sanata Kashim Shettima ya ce sun fuskanci hare-hare da-dama daga 'yan ya'addan Boko Haram a cikin shekarar nan.

‘Dan Majalisar dattawan na jam'iyyar APC ya jero ta’adin Boko Haram da aka yi a Borno, yace sau 2800 aka kawo masu hari daga watan Junairu zuwa Nuwamba.

Kashim Shettima ya yi wa Shugaba Buhari hannunka mai sanda cewa hafsun Soji sun gaza.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel