Rikicin kudancin Kaduna ya dade yana faruwa, Sheikh Gumi

Rikicin kudancin Kaduna ya dade yana faruwa, Sheikh Gumi

- Babban malamin musulunci na Kaduna, Sheikh Ahmad Gumi, ya fara shirye-shiryen kawo karshen rikicin Kaduna

- Shi da sauran malamai na addinin kirista masu daraja a jihar sun fara shirin a karkashin wata kungiya ta KHF

- A cewarsa, rikicin ya dauki lokaci mai tsawo, don haka suke so su hada karfi da karfe wurin ganin karshen rikicin

Babban malamin addinin musulunci na jihar Kaduna, Dr Ahmad Abubakar Gumi, ya ce rikicin kudancin Kaduna ya dauki lokaci mai tsawo, Daily Trust ta wallafa.

A cewarsa, ya zama tilas mutanen kirki, maza da mata, su hada karfi da karfe wurin kawo karshen rikicin addinin.

Dr Gumi, wanda shine shugaban KHF ya fara shirin kawo karshen rikicin addini da ke addabar kudancin Kaduna, wanda yake hana cigaba da zaman lafiya.

Sheikh Gumi ya ce zaman lafiyar kudancin Kaduna zai shafi wasu sassan jihar, wanda zai kawo cigaba a Najeriya, saboda kowacce kabila tana da rassa a wasu jihohin.

KU KARANTA: Budurwar da ta bar saurayi talaka saboda mai kudi ta sha caccaka daga jama'a

Rikicin kudancin Kaduna ya dade yana faruwa, Sheikh Gumi
Rikicin kudancin Kaduna ya dade yana faruwa, Sheikh Gumi. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

Malamin ya ce 'yan Najeriya sun zura ido suna kallon shirye-shiryen yadda za a bullo wa rikicin. Kuma matsawar aka samu nasara, sauran bangarori na kasar nan za su koyi yadda za su gyara nasu rikice-rikicen.

Malamin ya lura da yadda gwamnati, shugabanni da sauran mutane suke iyakar kokarin ganin karshen wannan rikicin, kuma KHF za su mike tsaye wurin ganin karshen rikicin.

KU KARANTA: 'Yan arewa sun yi gagarumar asara da suka saka wa Buhari kuri'u, Kungiyoyi

Mambobin KHF sun hada da musulmai 22 masu daraja a idon al'umma da shugabannin kiristoci kamar, Apostle Emmanuel Nuhu Kure, Archbishop Buba Lamido, Bishop Timothy Yahaya, Rev. Prof. Moses Audi, Rev. Ishaya Adamu Jandogo, Bishop Julius Yakubu Kundi, Rev. Barnabas Dodo, Arch. Bishop Matthew Man-oso Ndagoso, Arch. Bishop Sunday Oga Idoko, Rev. Dr. Olatunbosun, Shola James da Mrs. Agatha Asabe Soji, duk suna cikin 'yan kungiyar.

Sauran 'yan kungiyar sun hada da Sheikh Abdulkareem Hashim, Sheikh Dr. Ahmad Abubakar Gumi, Malam Muhamamdu Kabir Alkasim, Mallam Tahir Baba Ibrahim, Mallam Yusuf Yakubu Alrigasiyyu, Sheikh Hamza Muhammad Lawal, Tukur Adam Almanna, Dr. Muhammadu Suleiman, Alhaji Mohammed Maruf Raji, Alhaji Sheriff Olutusin da Hajiya Fadila Musa.

A wani labari na daban, majalisar dattawa ta kira wani babban kwamishinan Birtaniya zuwa Najeriya a kan wani tsokaci da wani dan majalisar Birtaniya, Tom Tugendhat yayi a kan tsohon shugaban kasan Najeriya, Yakubu Gowon.

A ranar 23 ga watan Nuwamba, ana tsaka da wata muhawara a kan majalisar UK na korafin da 'yan Najeriya suka yi a kan hukunta jami'an tsaron da suke da hannu a kan kashe-kashen Lekki Toll Gate.

Ya zargi Gowon da kwashe rabin kudin CBN ya gudu dasu lokacin da ya bace.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel