Diezani Alison Madukwe ta zama Kwamishina a kasar Dominican Republic
Rahotanni sun fara bayyana a game da yadda tsohuwar ministan man Najeriya, Madam Diezani Alison-Madueke ta lallaba ta tsere daga Najeriya a daf da karshen mulkin Goodluck Jonathan.
Diezani Alison-Madueke wanda ake zargi da laiffufuka a Najeriya, ta samu takardar fasfo da ake ba manyan ‘yan kasa a hannun gwamnatin Dominican Republic bayan ta sauka daga kan mulki.
Jaridar Pulse ta ce bayan samun fasfo, Alison-Madueke wanda ta rike kujerar ministar mai a gwamnatin PDP tsakanin 2010 zuwa 2015, ta zama Kwamishina a kasar Dominican Republic.
Wasu takardu da su ka fito daga hukumar su ka fada hannun jaridar Pulse sun nuna cewa Diezani Alison-Madueke ta samu mukamin kwamishinar kasuwanci da hada-hada a kasar wajen.
Wani jami’in hukumar EFCC ya shaidawa jaridar cewa “Da wannan fasfo na musamman, (Diezani) ta samu Katanga daga damkar kowace hukuma da jami’an tsaro, har da Interpol.”
KU KARANTA: Sanata Nwaboshi ya jefi Ministan Neja-Delta da zargin cin kudin kwangila
Ya ce: “Kafin barin ofis a ranar 28 ga watan Mayu, 2015, ta shawo kan ta da Firayim Ministan kasar Dominica. Ta shiga-ta fita, aka nada ta Kwamishinar kasuwanci da kuma hada-hada.”
Alison-Madueke ta dare kan wannan kujera ne a ranar 1 ga watan Yuni, 2015. Kutun-kutun din da ta yi ya yi aiki, wata wasika da ta fito daga ofishin Firayamin Ministan kasar ta tabbatar da haka.
Majiyar ta ce “Bayan Firayim Minista Roosevelt Kerry ya ba Diezani Alison-Madueke takardar zama cikakkar ‘yar kasa, ya kuma ba ta kujerar Kwamishinar kasuwanci da zuba hannun jari.”
Da wannan takardu da fasfo har jami’an kasar Amurka ba su da hurumin cafke tsohuwar ministar Najeriyar. Sai dai wani hanzari ba gudu ba, takardun za su tashi aiki ne a cikin Mayun 2020.
A shafi na 32 na fasfon da aka ba Alison-Madueke, an bayyana ba ya halasta a kama ta. Haka zalika duk wanda ya mallaki wannan takarda zai zamu alfarma a duk kasar da ya samu kansa.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng