EFCC: Alkali ta bukaci ganin hujjar kama Alison-Madueke daga hannun AGF
- An koma kotu tsakanin hukumar EFCC da Diezani Alison-Madueke
- Hukumar ta roki a ba ta alfarmar taso keyar tsohuwar Ministar man
- Alkali ba ta rubuta sabuwar takardar da za ta bada iznin yin haka ba
A ranar Laraba, 28 ga watan Oktoba, 2020, babban kotun tarayya da ke Abuja ta ki yin na’am da rokon da EFCC ta ke nema a kan Diezani Alison-Madueke.
Punch ta ce EFCC ta na so a ba ta dama ta kamo tsohuwar ministar Najeriya, Diezani Alison-Madueke, wanda ake kyautata zaton ta na labe a kasar Ingila.
Alkali mai shari’a Ijeoma Ojukwu, ta yi fatali da rokon da hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa ta gabatar a gabanta.
KU KARANTA: Magu ya na so a damko masa Diezani Alison-Madueke
Ijeoma Ojukwu ta ki yin na’am da bukatar EFCC ne a dalilin gazawar ta na kin bayyana a gaban kotu kamar yadda aka bukata tun a cikin watan Yulin 2020.
Bayan jami’an EFCC sun ki bayyana a kotu, sai kuma su ka aiko Lauyansu, Farouk Abdullah, ya na neman alfarma wajen Alkali domin a cafko tsohuwar ministar.
Rahotanni sun bayyana cewa Mai shari’a Ojukwu ta nuna za ta iya ba hukumar takardar da ta ke bukata, amma sai ta samu hujja daga hannun Ministan shari’a.
“A ra’ayina takardar neman gurfana za su taimaka wa ofishin AGF wajen taso keyar wanda ake tuhuma.”
KU KARANTA: Diezani Alison Madukwe ta samu mukami a kasar waje
“A yau wanda ake kara ba ya kotu, ba tare da an bada wani dalili ba. Ana fada mani cewa ana tunanin wanda ake zargi ta na Birtaniya”
Alkalin ta ce hukuncin da ta ke yanke a kan Diezani Alison-Madueke a ranar 24 ga watan Yulin 2019 sun isa hukumar EFCC ta tasota a gaba har zuwa Najeriya.
A ranar Laraban nan ne kuma mu ka samu labari cewa an kai babban Jigon APC kuma tsohon gwamna, Bola Tinubu gaban kotu, takardun shari’a sun babbake.
Lauyan da ya shigar da kara ya ce takardun shari'ar sun kone kurmus a wajen zanga-zanga.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng