Yadda kashe-kashen da ake yi, ya ke jefa Najeriya cikin hadarin yunwa

Yadda kashe-kashen da ake yi, ya ke jefa Najeriya cikin hadarin yunwa

- Shugaban Jami’ar Al-Hikmah ya ce akwai yiwuwar ayi karancin abinci

- Noah Yusuf ya ce kashe manoman da ake yi zai iya jawo wannan bala’i

- Yusuf ya bayyana ambaliyar ruwa da rigingimu a matsayin wasu dalilan

Shugaban jami’ar Al-Hikmah, Ilorin, jihar Kwara, Farfesa Noah Yusuf, ya ce kisan da aka yi wa manoma, hadari ne ga samun isasshen kayan abinci.

Masanin ya ce bayan wannan kashe-kashe, za a ga tasirin ambaliyar ruwa da aka samu a wasu jihohi da kuma rikicin makiyaya da manoma da ake yi.

Farfesa Noah Yusuf yace wadannan abubuwa za suyi sanadiyyar jawo ci-baya ga nasarar da gwamnatin Muhammadu Buhari ta samu a harkar noma.

Tun ba yanzu ba kuma ana samun rashin jituwa tsakanin makiyaya da manoma, inda masu shuka ke zargin makiyaya da jawo masu asarar amfani.

KU KARANTA: Babu yunwa a Najeriya - Ministan noma

Hakan na zuwa ne bayan an samu ‘yan ta’addan Boko Haram sun kashe wasu manoma fiye da 40 a kauyen Zabarmari, karamar hukumar Jere, jihar Borno.

Yusuf ya bayyana wannan ne lokacin da ya yi hira da ‘yan jarida a garin Ilorin, jihar Kwara, wajen shirin bikin yaye wasu daliban da suka kammala karatu.

Shugaban jami’ar ta Al-Hikmah ya ce a shekarar nan za ayi bikin yaye dalibai ta kafar yanar gizo saboda annobar COVID-19 da ta takaita cakuduwar jama’a.

Farfesan ya koka game da halin da suke ciki, ya ce gwamnati ba ta ba makarantu masu zaman kansu gudumuwa ba duk da irin rawar da su ke taka wa.

Yadda kashe-kashen da ake yi, ya ke jefa Najeriya cikin hadarin yunwa
Farfesa Noah Yusuf: thenationonlineng.net
Source: UGC

KU KARANTA: Mun fi kowa noma shinkafa a Afrika - Nanono

A wannan shekara, Yusuf ya ce za su yaye dalibai 752, ciki akwai 18 da su ka samu matakin farko na Digiri. Jaridar The Nation ta fitar da wannan rahoto.

A watan shekaran jiya ne shugaba Muhammadu Buhari ya jaddada cewa gwamnatinsa za ta farfado da fannin noma domin samar da wadataccen abinci.

Shugaban kasar ya ce maida hankali kan bangaren noma zai rage dogaron da kasar ta ke yi a kan danyen mai, domin Najeriya za ta iya rika fitar da abinci waje.

Muhammadu Buhari ya bada shawara ga matasa masu jini a jika, da su dage sosai da aikin gona.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit Nigeria

Online view pixel