An sa Emefiele, El-Rufai a cikin masu magana wajen babban taron Gwamnoni

An sa Emefiele, El-Rufai a cikin masu magana wajen babban taron Gwamnoni

- Gwamnonin Jihohi za su yi wani zama a dalilin matsalar rashin tsaro

- Kungiyar NGF za ta zauna ne a Ranar Laraba bayan harin Zabarmari

- Gwamnan Kaduna da babban bankin CBN zasu yi jawabi wajen taron

Vanguard ta ce gwamnonin jihohi 36 na kasar nan a karkashin kungiyar NGF za su zauna a gobe, 2 ga watan Disamba, 2020, a dalilin sha’anin tsaro.

Babban makasudin wannan taro shi ne gwamnonin su fito da sabon tsari a game da harkar tsaro.

A halin yanzu ana fama da yawan hare-haren ‘yan bindiga, ta’addancin Boko Haram da garkuwa da mutane da ake yi a jihohi da-dama a Najeriya.

Ana cikin wannan yanayi sai ‘yan ta’addan Boko Haram suka kai hari a kauyen Zabarmari, jihar Borno, inda su kayi wa mutane har 43 yankan-rago.

KU KARANTA: Zulum ya jagoranci sallarg gawar mamatan Zabarmari

Lamarin rashin tsaro yana damun jihohin kasar. Wannan zama da za ayi a ranar Laraba shi ne karo na 22 da kungiyar gwamnonin za ta zauna.

Daga cikin batutuwan da za a tattauna a zaman gobe, akwai kudirin ruwa da ya kawo ce-ce-ku-ce da Ministan harkokin ruwa zai yi karin-haske a kai.

Bayan jawabi daga Suleiman Hussein Adamu, takwaransa a ma’aikatar shari’a, Abubakar Malami zai bayyana inda aka kwana kan kudin harajin hatimi.

Haka zalika babban gwamnan CBN, Godwin Emefiele da gwamna Nasir El-Rufai za suyi magana kan yadda ake yin ayyuka da kudin asusun fansho.

KU KARANTA: An samu ‘Yan bindigan da su ka yanka wuyan Malami a Benuwai

An sa Emefiele, El-Rufai a cikin masu magana wajen babban taron Gwamnoni
Kungiyar Gwamnoni Hoto: channelstv.com
Asali: Facebook

Darektar NGF, Asishana Bayo Okauru, ta ce za a fara taron ne da karfe 2:00 na rana, amma gwamnoni za su samu damar hallara ta kafar gizo kafin nan.

A ranar Litinin kun ji cewa kungiyar ta NAS ta bukaci ayi waje da duka hafsun sojoji, hakan na zuwa ne bayan an yi wa mutane 40 yankan rago, a Borno.

NAS ta fadawa mai girma Muhammadu Buhari cewa tun farko abin da ya kamata ayi bayan kisar mutum 100 a jihar ta Borno shi ne a sauke shugabannin tsaro.

Ba wannan ba ne karon farko da kungiya ko wasu mutane su ka fito su na kira ga gwamnatin tarayya ta cire Hafsun tsaron da suke kan kujera tun 2015.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel