Zabarmari: Fafaroma ya yi Allah-wadai da yankan ragon da aka yi wa Manoma
- Duniya ta na cigaba da yin tir da abin da Boko Haram ta yi a Borno
- Fafaroma Francis ya shiga cikin masu yi wa ‘Yan Najeriya ta’aziyya
- Shugaban darikar Kiristoci ya ce abin takaici ne ya faru a Zabarmari
Shugaban darikar katolika na mabiya addinin Kirista, Fafaroma Francis ya fito ya soki harin da ‘yan ta’addan Boko Haram su ka kai a jihar Borno.
Babban limamin na Rome ya soki harin ta’addancin ne a hudubar da ya saba yi a kowane mako.
“Ina so in tabbatar da addu’a ta ga Najeriya, inda cikin takaici, aka sake zubar da jini a harin ta’addanci.” Inji Jorge Mario Bergoglio a yau Laraba.
Kamar yadda TVC ta rahoto, Fafaroma ya kira abin da ya auku a garin Zabarmari, jihar Borno, kisan gilla daga ‘yan Boko Haram da ke tada kafar baya.
KU KARANTA: Majalisa ta yi wa Buhari rubdugu kan kisan gillar Zabarmari
Shugaban Katolikawan ya yi wa wadanda aka kashe addu’ar samun rahamar Ubangiji, sannan ya yi wa iyalan da su ka bari, ya roka wa ‘yan ta’addan tuba.
“Mu na rokon Ubangiji ya yi masu kyakkyawar tarba cikin amini, Ya ba danginsu dangana, Ya canza zuciyar wadanda su ke ta’adin da ke bata masa suna.”
A wannan harin, ‘yan ta’addan sun aika manoman ta hanyar yanka wuyayansu a cikin gonaki.
Maganar Fafaroman ya zo ne kwanaki bayan ‘yan ta’addan sun shiga har gonakin wasu Bayin Allah fiye da 40, sun yi masu yankan rago a garin Jere.
KU KARANTA:
Jorge Mario Bergoglio ya yi amfani da wannan dama ta yau, ya tuna da wasu Kiristoci masu yada manufa da aka kashe shekaru 40 da aka kashe a yakin El Salvador.
Kun ji cewa kungiyar NAS ta tofa albarkacin bakinta a kan harin da aka kai a Zabarmari, karamar hukumar Jere. NAS ta ce harin yana cikin mafi muni Boko Haram.
Wannan kungiya ta ce ya kamata shugaba Muhammadu Buhari ya sauya hafsun sojojin kasar nan.
Shugaban NAS, Abiola Owoaje ne ya fitar da wani jawabi da ya yi wa taken “Kisan gillar da ‘yan ta’adda su ka yi wa manoman shinkafa 34 a garin Zabarmari” a jiya.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng