Zabarmari: Babu tsaro a gida da daji inji Kungiyar Jama’atu Nasril Islam

Zabarmari: Babu tsaro a gida da daji inji Kungiyar Jama’atu Nasril Islam

-Jama’atu Nasril Islam ta ce jama’a suna rayuwa yanzu cikin firgici a Najeriya

-Kungiyar JNI tace a halin yanzu babu tsaro a gidaje, gonaki da daji a kasar nan

-Sakataren kungiyar Jama’at Nasril Islam ya soki harin da aka kai a Zabarmari

Kungiyar Jama’atu Nasril Islam da Mai alfarma Sarkin Musulmi, Sa’ad Abubakar III ya ke jagoranta ta koka game da lamarin tsaro yau a kasar nan.

Jaridar Punch ta rahoto kungiyar Jama’atu Nasril Islam ta na kira ga shugaba Muhammadu Buhari ya daina yi wa jama’a zakin-baki a kan sha’anin tsaro.

JNI ta ke cewa a halin yanzu mutanen Najeriya suna bukatar gwamnatin tarayya ta samar da zaman lafiya ne ba ayi ta fitar da jawabai na sukar ‘yan ta’adda ba.

Jaridar tace Jama’atu Nasril Islam ta bayyana wannan ne a wani jawabi da Sakatare Janar dinta, Dr. Khalid Aliyu ya fitar a ranar Laraba daga garin Kaduna.

KU KARANTA: Sanatoci sun yi kaca-kaca da Buhari kan matsalar tsaro

Dr. Khalid Aliyu ya yi wa jawabin na sa take da: ‘Press release: Requiem for Zabarmari’, a matsayin ta’aziyya ga mutane 40 zuwa 1100 da aka rasa a jihar Borno.

“Har ila yau, mu na sake kira ga gwamnatin tarayya ta tashi tsaye, ta yi abin da ya wuce maganar fatar-baki na sukar (ta’addanci) da aka saba.” Inji kungiyar.

JNI ta ce: “Dole a daina wannan, ‘Yan Najeriya suna matukar bukatar ganin an dauki mataki.”

Kungiyar addinin ta ce yanka mutane fiye da 40 a gonakinsu da aka yi a kauyen Zabarmari, garin Jere, ba tare da jami’ai sun yi wani abu ba, abin ayi tir ne.

KU KARANTA: A tsige Hafsun soji - NAS ga Buhari

Zabarmari: Babu tsaro a gida da daji inji Kungiyar Jama’atu Nasril Islam
Sarakuna a Aso Villa Hoto: Abuja_Facts
Asali: Twitter

Aliyu ya koka da halin da ake ciki na garkuwa da mutane, fyade, rashin aiki da sauran ta’addanci.

“Yan Najeriya suna cikin firgici, babu zaman lafiya ko ta ina: gidaje, gonaki, kan tituna. Tsageru na rike da garuruwa, su ne ke da iko.” Inji JNI a jawabin na ta.

Dazu kun ji cewa Fafaroma Francis ya yi Allah-wadai da yankan ragon da aka yi wa Manoma 43 a garin Zabarmari. Shugaban Katolikan ya yi maganar ne a jiya.

Fafaroman ya yi wa ‘Yan Boko Haram da su ka kai hari a gonakin Bayin Allah addu’ar samun shiriya, sannan ya roki Ubangiji ya ba iyalan mamatan hakuri.

Hakan na zuwa ne a lokacin da gwamnonin kasar nan su ke cewa matsalar tsaro ya fi karfin sojoji.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel