Trump: “Muna neman tazarce, idan bai yiwu ba, sai mun hadu nan da shekarar 2024”
- Donald Trump ya nuna cewa zai iya sake neman mulki a shekarar 2024
- Shugaban Amurkan mai barin-gado bai yarda ya fadi zaben da aka yi ba
- Trump ya ce idan tazarce bai yiwu ba, to sai dawo nan da shekaru hudu
A ranar Laraba, 2 ga watan Disamba, 2020, mu ka ji cewa Donald Trump ya soma bijiro da maganar sake jarraba wata sa’arsa a siyasar kasar Amurka.
Jaridar The Guardian ta fitar da rahoto cewa, shugaban Amurka Donald Trump yana tunanin sake neman takarar shugaban kasa a zabe mai zuwa na 2024.
Donald Trump wanda ya sha kasa a zaben da aka yi kwanan nan a hannun Joe Biden, yana da burin ganin ya kara shekaru hudu a fadar White House.
Trump ya kawo maganar sake tsaya wa takara ne a wajen liyafar da ya shirya a fadar shugaban kasa a ranar Talata da yamma, kamar yadda jaridar ta fada.
KU KARANTA: Shugabannin Amurka 10 da su ka fadi a zaben tazarce
An rahoto shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya na mai fada wa cincirindon jama’an da su ka halarci wannan biki: “Wadannan shekaru hudu sun yi kyau.”
“Mu na kokarin mu sake yin wasu shekaru hudu.” Inji Trump wanda ya sha kashi a zaben bana.
Wadanda su ka halarci wannan babbar liyafa da aka shirya a fadar shugaban kasar sun hada da jiga-jigan jam’iyyar Republican mai rike da mulki a Amurka.
Shugaban ya kare kalamansa da cewa: “Idan kuma ba haka ba, sai na gan ku nan da shekaru hudu.”
KU KARANTA: Trump ya yarda da kayi
Daya daga cikin manyan jam’iyyar Republican a Oklahoma, Pam Pollard, ya dauki Trump kai-tsaye a dandalin Facebook a lokacin da yake wannan magana.
Kwanakin baya mun kawo maku rahoto cewa Donald Trump ya na la’akari da fitowa takara a 2024, bayan jam'iyyar Democrat mai hamayya ta tika shi da kasa.
Wasu tsofaffin Hadiman Shugaban kasar sun bijiro masa da batun tarar gaba domin ya tsira da mutuncinsa, a lokacin da yake watsi da nasarar da Joe Biden.
Tun da Donald J. Trump ya sha kashi a zaben bana, ya na da damar ya fito takara a nan gaba.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng