Shugabannin Amurka 10 kacal suka fadi a zaben tazarce a tarihi, Trump ya zama na 11 (Ga jerinsu)

Shugabannin Amurka 10 kacal suka fadi a zaben tazarce a tarihi, Trump ya zama na 11 (Ga jerinsu)

- Gabanin yau, Shugabannin kasar Amurka 10 kadai suka ta fadi a zabe a tarihin kasar

- Zabubbuka sun nuna cewa da kamar wuya Trump ya lashe zaben bana saboda yadda ya jagoranci yaki da cutar COVID-19

- Trump ya sha kaye hannun Biden a kuri'un da aka kawo yanzu a jihohi 24

A tarihin Amurka, shugabannin kasa suna samun nasarar tazarce bayan karewar wa'adinsu na farko saboda irin ayyukan da suka yi.

Amma ba haka ya faru da Donald Trump ba saboda lokacin da ya kaddamar yakin neman zabensa a 2019, maki 43% kadai ya samu, cewar Gallup.

Trump ya samu nasarar lashe zabe a jihohi 22 yayinda Biden ya lashe a jihohi 25 kuma har yanzu ba'a kammala kirga a jihohi 3 ba (Georgia, Alaska, da North Carolina)

Biden ya kayar da Trump a jihohin da ya ci a zaben 2016. Jihohi irinsu Michigan, Wisconsin, Pennsylvania da Arizona.

Shugabannin Amurka 10 kacal suka fadi a zaben tazarce a tarihi, Trump ya zama na 11 (Ga jerinsu)
Shugabannin Amurka 10 kacal suka fadi a zaben tazarce a tarihi, Trump ya zama na 11 (Ga jerinsu)
Asali: Getty Images

Ga jerin tsaffin shugabannin Amurka da suka fadi a zaben tazarce:

1. John Adams (1797-1801)

2. John Quincy Adams (1825-1829)

3. Martin Van Buren (1837-1841)

4. Grover Cleveland (1885-1889)

5. Benjamin Harrison (1889-1893)

6. William Howard Taft (1909-1913)

7. Herbert Hoover (1929-1933)

8. Gerald Ford (1974-1977)

9. Jimmy Carter (1977-1981)

10. George H.W. Bush (1989-1993)

11. Donald Trump (2016-2020)

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel