Buhari: Kisan manoma a Zabarmari ya ci ace ka sauke Hafsun Sojoji inji NAS
- Kungiyar NAS ta tofa albarkacin bakinta a kan harin da aka kai a Zabarmari
- NAS ta ce wannan hari yana cikin mafi muni da aka tani gani daga Boko Haram
- An ba shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sauya hafsun sojojin kasar nan
Jaridar Vanguard ta ce kungiyar NAS ta kasa, ta shiga sahun ‘yan Najeriyan da su ke ganin ya kamata a sauke shugabannin hafsoshin tsaron kasar nan.
Hakan na zuwa ne bayan an tabbatar da mutuwar wasu manoma a hannun ‘yan ta’addan Boko Haram a garin Zabarmari, karamar hukumar Jere, Borno.
Shugaban NAS, Abiola Owoaje, ya fitar da wani jawabi da ya yi wa taken “Kisan gillar da ‘yan ta’adda su ka yi wa manoman shinkafa 34 a garin Zabarmari.”
KU KARANTA: Mutanen da aka kashe a Borno sun zarce 100 - UN
A cewar Abiola Owoaje, wannan sabon hari da aka kai, ya na cikin mafi munin ta’adin da ‘yan ta’addan Boko Haram suka taba yi tun kafuwarsu a tarihi.
Owoaje ya ke cewa halin da ake ciki a kasar nan ya na kara zama abin ban tsoro, sannan babu alamun kawo karshen wannan mummunan lamarin ta’addanci.
Kungiyar ta yi kira ga hukumomin Najeriya su kara kokari tare da fito da dabarun kawo zaman lafiya da yi wa sha’anin tsaro garambawul domin kare al’umma.
NAS a jawabin na ta, ta ce: “A game da haka, ya kamata gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta yi hobbasa ya canza shugabannin hafsoshin tsaro.”
KU KARANTA: Kungiyar CNG ta yi kaca-kaca da Gwamnoni da Shugaba Buhari
Mista Owoaje ya na ganin cewa ana bukatar sababbin zubin hafsun sojoji da za su gyara tsaro.
“Zabin ya zama an yi la’akari da tsantsar cancantar aiki, ta yadda za a shigo da sababbin dabaru da tunani musamman wajen tattaro bayanan shawo kan Boko Haram.”
A daidai lokacin da NAS ta ke wannan magana, mutane a Twitter sun fito suna wannan kira.
A ranar Lahadi ne ku ka ji cewa Sanatan APC, Mohammed Ali Ndume yana nadamar sukar Goodluck Jonathan bayan shekaru biyar da barinsa karagar mulki.
‘Dan majalisar ya ke cewa ya gane kuskurensa, kuma masu sukar Jonathan suna yabonsa a yau.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng