Buhari: Gwamnatin Tarayya ta gaza tsare ran ‘Yan Najeriya inji Majalisar Dattawa

Buhari: Gwamnatin Tarayya ta gaza tsare ran ‘Yan Najeriya inji Majalisar Dattawa

- ‘Yan Majalisar Dattawa sunyi Allah-wadai da harin da aka kai a Garin Zabarmari

- Sanata Ahmad Babba Kaita ya ce gwamnatin Buhari ta gaza inganta harkar tsaro

- Sanatoci sun ba Gwamnatin Tarayya shawara kan yadda za a samu zaman lafiya

A ranar Talata, majalisar dattawa ta fito ta yi magana game da kisan gillar da ‘yan ta’addan Boko Haram su kayi wa wasu manoma a jihar Borno.

Majalisar dattawan kasar ta soki Muhammadu Buhari na gaza tsare ran ‘yan Najeriya, inda su kai kira a gare shi ya yi garambawul ga sha’anin tsaro.

Jaridar The Nation ta ce ‘yan majalisar tarayyan sun tsaida adadin mutanen da aka kashe a Borno a kan 67, a maimakon 43 da gwamnati take fada.

Sanata Kashim Shettima ya fara kawo maganar da sauran ‘yan majalisa duk suka mara masa baya. Daga cikinsu har da Ali Ndume daBabba Kaita.

KU KARANTA: Akwai yiwuwar har nan da shekara 20 ba a gama yaki da ta’addanci ba

Bayan tattaunawar Sanatocin, za a kai wa shugaban kasa matsayar da aka cinma a kan mummunar kisan gillar da aka yi wa mutanen garin Zabarmari.

Daga cikin abubuwan da majalisa take so Buhari ya yi shi ne: tsige hafsun sojoji, a rika biyan jami’an tsaro hakkokinsu, sannan a binciki barnar da ake yi.

Yi wa sha’anin tsaro garambawul, daukar ‘yan sa-kai 10000 aiki, hada-kai da sauran kasashe, tare da duba abin dake haddasa rashin tsaro suna cikin shawarwarin.

Sanata Ahmed Baba Kaita mai wakiltar Arewacin Katsina ya ce kokarin da shugaba Muhammadu Buhari yake yi bai samar da wani nasara ba har zuwa yau.

KU KARANTA: Jawabi daga bakin tawagar da Muhammadu Buhari ya aika Zabarmari

Buhari: Gwamnatin Tarayya ta gaza tsare ran ‘Yan Najeriya inji Majalisar Dattawa
Shugaban Majalisar Dattawa Hoto: pmnewsnigeria.com
Source: Facebook

A cewar ‘Dan majalisar na mazabar shugaban kasar, duk da kokarin Mai girma Buhari, akwai sauran jan aiki da ke gaban gwamnatinsa a kan harkar tsaro.

“Lokaci yayi da za mu fadi gaskiya. ‘Yan Najeriya ba za su cigaba da yarda da wannan ba.” Inji Babba Kaita, kamar yadda jaridar The Cable ta fitar da rahoto a jiya.

Ku na da labari a yau ne ake sa ran gwamnonin Jihohi za su yi wani zama a dalilin matsalar rashin tsaro da ke addabar musamman yankin Arewacin Najeriya.

Kungiyar NGF ta gwamnonin jihohi 36 za ta zauna a Ranar Laraba da rana, bayan harin da 'yan ta'addan Boko Haram su ka kai a garin Zabarmari, dake jihar Borno.

Bayan nan Gwamnan Kaduna da gwamnan babban bankin CBN zasu yi jawabi wajen taron.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit Newspaper

Online view pixel