Ina kira ga mahukunta su dauki mataki kan rashin tsaro da arewa ke fama dashi, Rahama Sadau

Ina kira ga mahukunta su dauki mataki kan rashin tsaro da arewa ke fama dashi, Rahama Sadau

- Jarumar Kannywood, Rahama Sadau ta magantu a kan wasu tarin matsaloli da ke addabar kasar a yanzu

- Rahama ta yi kira ga mahukunta a kan su dauki matakin gaggawa kan matsalar rashin tsaro da ke damun arewacin kasar

- Ta kuma bayyana shekarar 2020 a matsayin wacce ke cike da tarin kalubale kama daga korona, karyewar tattalin arziki da kuma rashin tsaro

Shahararriyar jarumar masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Rahama Sadau, ta yi martani a kan batutuwan da suka addabi kasar a yanzu.

Jarumar ta bayyana cewa wannan ta zo da abubuwa da dama na kalubale wanda suka hada da Korona da matsalar tattalin arziki da kuma matsalar tsaro.

Rahama ta kuma yi Allah-wadai da abinda ya faru a yankin arewacin kasar inda tayi kira ga mahukunta a kan su yi wani abu a kai cikin gaggawa.

Ina kira ga mahukunta su dauki mataki kan rashin tsaro da arewa ke fama dashi, Rahama Sadau
Ina kira ga mahukunta su dauki mataki kan rashin tsaro da arewa ke fama dashi, Rahama Sadau Hoto: rahamasadau
Asali: Instagram

Legit.ng ta tattaro cewa jarumar wacce ta bayyana wannan wata ta Disamba a matsayin watan zagayowar haihuwarta ta kuma nemi a dauki mataki kan matsalar cin zarafin mata.

KU KARANTA KUMA: Kisan Borno: Lokacin sauya tsarin tsaro yayi, Lawan ga Gwamnatin tarayya

Ga yadda ta wallafa a shafinsa na Instagram:

"An shiga watan Disamba.. watan haihuwata kuma watan karshe na shekara.

"Wannan shekara ta 2020 ta zo da manyan kalubale, farko Covid-19, na biyu koma bayan tattalin arziki sannan na uku rashin tsaro. Wadannan lamura sun zurfafa cin zarafin mata wadanda ke shanye radadin rikicin.

"Rashin tsaron na muke fuskanta yanzu haka a arewacin Najeriya abun damuwa ne kuma ya kamata a dauki matakin gaggawa. Amfanin wannan rayuwa shine yi wa al’umma hidima, amma ta yaya za mu yi wa rayuwa hidima bayan mun rasa duk wani tausayi na rai? Hakan jahilci ne tsantsa.

"Ina kira ga hukumomin da suka kamata a kan su dauki mataki sannan su karemu daga hauhawan rikici kan mata sannan su kawo karshen rashin tsaro a Najeriya."

KU KARANTA KUMA: Karin bayani: Majalisar wakilai ta aika sammaci ga Buhari kan kisan Zabarmari

A wani labarin, Kungiyar ta’addanci ta Boko Haram ta dauki alhakin harin da aka kai garin Zabarmari na jihar Borno.

A wani bidiyo da ta saki a ranar Talata, kwamandan kungiyar ya yi jawabi a faifan inda ya bayyana cewa sun aiwatar da kisan kiyashin ne domin rama kisan mambobinsu da sojojin Najeriya suka yi.

Kungiyar ta gargadi yan farar hula da su guji yin leken asiri a kansu, shafin HumAngle ta wallafa a Twitter.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng