Bayan neman yafiyar gwamnatin Ganduje: Kotu ta sallami shari’ar Naziru M. Ahmad

Bayan neman yafiyar gwamnatin Ganduje: Kotu ta sallami shari’ar Naziru M. Ahmad

- Kotu ta sallami shari'ar da take yi tsakanin Naziru M. Ahmad da gwamnatin jihar Kano

- Wannan ci gaban na zuwa ne bayan sarkin wakar ya nemi yafiyar gwamnatin Abdullahi Ganduje

- An dai tuhumi shahararren mawakin ne da sakin wata waka tun ba a kai ga tantance ta ba

Wata kotun majistare da ke zama a jihar Kano ta sallami shari’ar shahararren mawakin nan na masana’atar Kannywood, Naziru M. Ahmed.

Hakan ya biyo bayan neman yafiyar gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje na jihar da mawakin yayi, sashin Hausa na BBC ta ruwaito.

Kotun wacce mai shari’a Aminu Gabari ke shugabanta, ta rufe shari’ar sarkin wakar kan laifin fitar da wata waka ba tare da hukumar tace fina-finai ta Kano ta tantance ta ba.

Bayan neman yafiyar gwamnatin Ganduje: Kotu ta sallami shari’ar Naziru M. Ahmad
Bayan neman yafiyar gwamnatin Ganduje: Kotu ta sallami shari’ar Naziru M. Ahmad Hoto: sarkin_wakar_san_kano
Asali: Instagram

Hakan ne ya sa a watan Satumban 2019 aka kama Naziru Sarkin Waka amma daga bisani kotun ta sake shi bayan ya cika ka’idojin belin da kotun ta shimfida masa.

Sai dai a farkon watan Nuwamba, kotun ta soke belin da aka bai Naziru inda ta shimfida masa wasu sababbin ka’idojin belin.

KU KARANTA KUMA: Boye matar aure: Wata kotu a Kano ta bukaci Rarara da ya bayyana a gabanta

Daga nan ne ta aike da shi gidan yari saboda rashin cika sharudan a kan lokaci, duk da cewa an gindaya masa su ne a kurarren lokaci, kamar yadda ya fadi.

A zaman kotun na ranar Talata, lauyan gwamnatin Kano, Barista Wada Ahmad Wada ya gabatar da wata takardar bayar da hakuri ga gwamnatin jihar wadda ya ce daga hannun Naziru ta fito.

A cikin takardar, wadda Sarkin Waka ya rubuta ta zuwa ga Kwamishinan labarai na jihar, ya ce "Ni Naziru M. Ahmed ina bayar da hakuri matuka bisa zargin da aka yi mini kuma ina dansanin abin da hakan ya haifar."

Mawakin ya kara da cewa ya bayar da hakurin ne bayan masu ruwa da tsaki sun tsoma baki a cikin lamarin.

Lauyan Naziru, Barista Sadik Sabo Kurawa, ya ce sun cimma wannan matsaya ce sakamakon fahimtar junan da aka samu daga bangarorin biyu.

"Abin da ya faru a yau shi ne da ma an samu daidaituwa tsakanin bangaren gwamnati da na wanda ake kara, shi ya sa suka zo yau suka kawo karshen tuhume-tuhumen da ake yi masa suka wanke shi daga ciki," in ji shi.

KU KARANTA KUMA: Matashin da ke samun 20,000 a wata ya siya wa budurwarsa abincin 4,500

Daga nan ne Mai Shari'a Aminu Gabari ya sallami Naziru M. Ahmed sannan aka rufe shari'ar baki baya.

A wani labarin, Shahararriyar jarumar masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Rahama Sadau, ta yi martani a kan batutuwan da suka addabi kasar a yanzu.

Jarumar ta bayyana cewa wannan ta zo da abubuwa da dama na kalubale wanda suka hada da Korona da matsalar tattalin arziki da kuma matsalar tsaro.

Rahama ta kuma yi Allah-wadai da abinda ya faru a yankin arewacin kasar inda tayi kira ga mahukunta a kan su yi wani abu a kai cikin gaggawa.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel