Oby Ezekwesili tana so a duba lafiyar kan Buhari ko ya cancanci ya rike Najeriya

Oby Ezekwesili tana so a duba lafiyar kan Buhari ko ya cancanci ya rike Najeriya

- Oby Ezekwesili tana so a samu Malaman kiwon lafiya su duba kwakwalwar Buhari

- Tsohuwar Ministar ta ce Mutanen kasa suna da damar sanin lafiyar shugaban na su

- Ezekwesili ta bijiro da wannan magana ne ganin yadda ake ta fama da matsalar tsaro

A ranar Talata, 1 ga watan Nuwamba, 2020, wata tsohuwar Ministar ilmi, Oby Ezekwesili ta nuna shakkunta game da lafiyar shugaban Najeriya.

Rahotanni sun ce Madam Oby Ezekwesili ta bukaci ayi wa lafiyar kwakwalwa da jikin shugaban kasa Muhammadu Buhari binciken kwa-kwaf.

Tsohuwar ‘yar takarar shugaban kasar ta bukaci ayi wannan ne domin al’ummar Najeriya su san ko shugaban kasar na su ya na da koshin lafiya.

KU KARANTA: Buhari ya nada sabuwar Shugabar NAPTIP

Ezekwesili ta fito ta yi wannan bayani ne a dandalin sada zumunta a shafinta na Twitter, @obyezeks.

A cewar Oby Ezekwesili, halin da ake ciki yanzu a Najeriya na rashin tsaro, ya ci ace an tashi an san lafiyar shugaban kasa Muhammadu Buhari.

“Ina tunani a wannan lokaci da kuma mummunan halin rashin tsaro da kasar nan take ciki, dole a hakura da maganar sirri, mutanen kasa suna da hakkin sanin halin lafiyar shugaban kasa Muhammadu Buhari.”

“Dole mu duba lafiyar jiki da kwakwalwar shugaban kasar domin sanin ko ya na da ikon cigaba da sauke nauyin da ke kansa na gudanar da aikin ofishin shugaban kasa.” Inji Oby Ezekwesili.

KU KARANTA: Gumi ya ce Buhari ya yi murabus

Oby Ezekwesili tana so a duba lafiyar kan Buhari ko ya cancanci ya rike Najeriya
Oby Ezekwesili Hoto: edition.cnn.com
Asali: UGC

Ta ce: “Mutanen kasa za su iya tursasa wa a kafa kwamiti mai zaman kansa, da zai taimaka mana da yi wa shugaban kasar gwaji domin sanin halin lafiyar da yake ciki.”

Shugabar tafiyar #BBOG ta ce kwamiti na dabam ya kamata ya yi wannan aiki, ba likitocin fadar shugaban kasa ba, ta ce ba za a yarda da ma’aikatan gwamnati ba.

A zaman da aka yi a ranar Talatar nan, Majalisar Dattawa ta tsaida matsaya cewa gwamnatin tarayya ta gaza tsare rai da dukiyoyin ‘Yan Najeriya a shekarun nan.

‘Yan Majalisar Dattawa sunyi Allah-wadai da harin da aka kai a Zabarmari, jihar Borno. Wadanda suka koka sun hada tsohon gwamnan Borno, Kashim Shettima.

Sanata Ahmad Babba Kaita ya yarda gwamnatin nan ta su ta APC ta gaza inganta harkar tsaro a kasa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel