Bode George: Saboda in yi wa Tinubu ritaya zan tsaya takarar Shugaban kasa

Bode George: Saboda in yi wa Tinubu ritaya zan tsaya takarar Shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban PDP na kasa, Olabode George, ya sha alwashin kawo karshen burin da ake rade-radin Bola Tinubu ya na yi na neman shugaban kasa.

A wata hira da Cif Olabode George ya yi da Jaridar The Sun, a karshen makon nan, ya bayyana cewa burinsa shi ne ya yi wa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ritaya a 2023.

Bode George ya yi wa jigon jam’iyyar APC mai mulki, Bola Tinubu barazana da cewa zai sha kallo a zaben 2023, domin zai kawo karshen rayuwar siyasarsa a zaben mai zuwa.

‘Dan adawar ya shaidawa ‘yan jarida cewa: “Daga cikin dalilan da su ka sa na shiga takarar shugaban kasan 2023 shi ne domin in tsaida Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.”

“Idan aka kai takarar shugaban kasa zuwa Kudu maso Yamma a 2023, kuma Bola Tinubu ya shiga takarar, ba wai zan kara da shi ba ne, a'a zan taka masa burki ne.”

KU KARANTA: Shugaba Buhari ba zai yi Tinubu a zaben 2023 ba - Yariman-Bakura

Bode George: Saboda in yi wa Tinubu ritaya zan tsaya takarar Shugaban kasa
Saboda Tinubu Bode George ya ke son ya yi takarar Shugaban kasa
Asali: UGC

Bode George ya kara da cewa: “Asiwaju Bola Tinubu ya tuna cewa Najeriya ta fi karfin Mazabarsa, ba Garin Legas ba ce inda Tinubu da jam’iyyar APC su ke ta murde zabe.”

Tun a farkon bana, fitaccen ‘Dan siyasar ya fito ya bayyana niyyarsa na tsayawa takarar shugaban kasa a zabe mai zuwa, ko da dai ba a fadi yankin da za a ba takara ba.

George wanda ya na cikin daya daga cikin kwamitin amintattun na jam’iyyar PDP, ya yi magana game da gwamnatin Buhari da sha’anin tsaro a wannan hira da ya yi jiya.

A na sa ra’ayin, ba ya ganin cewa akwai wadanda su ka killace shugaban kasa Muhammadu Buhari, a matsayinsa na tsohon Soja, har su ka hana shi yin aikin da ya kamata.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel